Mai daukar nauyin jama'a a cikin mutane

  • manzon Allah (salati da tsirar Allah su tabbata agareShi) Ya ce: (kotankwacin mutane tamkar rakuma dari ne; wadanda da wuya ka samu wanda za'a iya hawa). Bukhari da muslim suka ruwaito shi. Ma'anar hadisin: a cikin rakumi dari, da wuya ka samu wanda za' a iya hawa; saboda wanda za'a iya hawa shine mai saukin kai, mai mika wuya. Haka ne ma cikin mutane dari da wuya ka samu daya, wanda ya cancanci a abukancce shi; wanda yake taimaka wa abokin sa, kuma yake da saukin kai. Kurdubi yana cewa: abinda ya yi daidai da wannan misali shine mutun mai kyauta, mai daukar nauyin jama'a, mai taimaka masu, mai wuyar samuwa, tamkar rakumi mai daukar nauyin jama'a a cikin rakuma masu yawa. Haka kuma ibn Battal yana cewa: ma'anar hadisin: mutane suna da yawa, amma wanda jama'a suke yarda da su kadan ne. ka diba: fathul bari 11/335.
  • : Hausa
  • : 7035
  • : [ 3504 ] .. http://islam-love.com/ha/img/306/download