Dangogin ziyarar kaburbura da hukunce hukuncen da suka shafi haka:


Da sunan Allah mai rahama, mai jin kai

 

Dangogin ziyarar kaburbura da hukunce hukuncen da suka shafi haka:


*maziyarcin makabarta baya futa daga cikin halaye guda hudu:


- Hali na farko: ya kasance mai rokawa mamata gafarar Allah da rahamarSa; zai yi wa mamacin adu'a kuma ya roka masa gafarar Allah, shi kuma ya dau izna, ya kuma tuna makomarsa, zuciyarsa ta wa'aztu; wannan ita ce ziyara da shari'a ta yi umarni da ita.


-Hali na biyu: ya je makabarta, ko wani kabari na musamman, domin ya yiwa kansa ko wanin sa adu'a, yana mai kudurta cewa adu'a a makabarta ko a wajen wani kabari na musamman ta fi karbuwa; to wannan bidi'a ce abin ki mutuka.
- Hali na uku: ya roki Allah a wjen kabarin, yana mai neman tsani da jahi ko hakki ko darajar mai wannan kabari; tamkar ya ce: Allah ina rokon ka da jahi ko matsayin wane a wajen ka, ka biya mani bukata ta; to wannan bidi'a ce haramtatta; domin hanya ce zuwa ga shirka.
- Hali na hudu: ya kasance yana mai rokon mamatan, ko mamaci koma bayan Allah ma daukaki; tamkar ya ce: ya waliyin Allah, ko ya annabin Allah ... ina rokon ka ka yi mani wadata, ko ka bani kaza, ko abinda ya y i kama da haka; to wannan shirka ne babba.

 

  • Littafin da aka ciro wannan bayani: taudhihul ahkam min bulughil maram Wallafar: sheik Abdullah ibn Abdirrahman Al Bassam; member a cikin commitin manyan malamai na kasar saudiya.