Daga cikin manya manyan ayukkan manzon Allah


 

Daga cikin manya manyan ayukkan manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi)

 

Allah (madaukaki) Yana cewa a cikin suratul taubah - game da manzon Shi da Ya zaba, Ya kuma sabkar maSa da Alkur' ani mai girma; domin Ya isar da sako na karshe ga mutane -: « 128. Lalle ne, haƙĩƙa, Manzo  daga cikinku yã je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwaɗayi ne sabõda ku. Ga muminai Mai tausayi ne, Mai jin ƙai ».

 

A cikin fadar Allah « daga cikinku » a kwai dalili dake nuni game da karfin alakar da ke da kwai tsakanin wannan annabin da dukkan jinsi na bani adama; Shi wannan manzon daga cikin su yake, alakar Shi da su alakar mutun da mutun ce; domin haka sakon Shi ya kasance rahama ne ga dukkan halittu; Allah Yana cewa:  « 107. Kuma ba Mu aike ka ba fãce dõmin wata rahama ga talikai » [suratul anbiya'i].

Kuma kayi tunani –domin ka san yanda manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) Yake kaunar ganin dukkan mutane sun muslunta; ba dan kome ba sai dan tausayi da rahama gare su- ka yi tunani game da fadar Allah a cikin suratul kahfi : « 6. To, kã yi kusa ka halaka ranka a gurabbansu, wai dõmin ba su yi ĩmãni da wannan lãbãri ba sabõda baƙin ciki » .

Dan haka Ya tsaya, tsayin daka yana kira zuwa ga Allah da ikhlasi, tare da rahama da tausayin wadanda Yake kira.

Manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) Ya kwatanta halin Shi a cikin kiran Shi zuwa ga Allah Yana mai cewa: "lalle kwatankwacina game da mutane (da nake kira ), kamar mutun ne da ya fura wuta; yayin da ta haskaka kyewayen ta …. sai kwari suka kasance suna kokarin fadawa cikin wannan wutar, sai ya kasance yana hana su fadawa cikin ta, tare da cewa suna rinjayar shi, suna fadawa; dan haka Ni mai kama ku ne ta ta madaurin wando; domin kar ku fada cikin wuta, alhali kwa mutane suna durmiya cikibukhari ne ya ruwaito wannan hadisin.

Ma'anar hadisin shine: manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) Yana kama mutane ta madaurin wando dan kar su fada wuta …. Kamar mai hana kwari daga fadawa wuta yayin da su ka ga hasken ta;  su kuma suna ma su rinjayar su suna zuwa wajen ta har kuma ta toya su. Shi ma manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) yana nisantar da su daga wannan wuta domin kar su fada ciki.

Hakika manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) ya kasance mai rikon mutane ne; domin Ya nisantar da su daga dukkan abin da zai cutar da su a duniya da lahira, amma duk da haka mutane da yawa suna zuwa ga sharri.

manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) Ya kasance mai tausayi ne da jin kai, tare da kokarin ceto mutane daga dukkan abin da zai cuce su; domin su samu aljanna ranar kiyama, kuma su kubuta daga wuta; dan haka rayuwar shi ta kasance cike da manya manyan ayukka wadanda ke tabbatar da cewa lalle Shi annabi ne, kuma Shine shugaban ''yan Adam.

Yana daga cikin manya manyan ayukkan Shi:

Kira zuwa ga tauhidi ( kadaitar da Allah da bauta ) ; tauhidi kwa shine sababi na rayuwa ta hakika, tare da kwancin hankali da sa'ada; wanda ya yi imani da Allah a matsayin ubangijin shi wanda ba shi da abokin tarayya, kuma ya bauta masa ba tare da hada Shi da abokin tarayya ba, ba ya bin wata hanya da ba tashi ba, kuma ba ya bin umarni da hani na wanin Shi; to lalle wannan zai rayu rayuwa cikin nitsuwa; domin ya tabbatar da kadaita Allah yayin da ya meka wuya gare Shi; dan haka sakamakon shi shine samun dandano mai dadi na tsayuwa akan tafarkin Allah, tare da samun yakini da sani na hakika, da tsinkaye mai kyau, da ganin hanya ta daidai, da daukaka; domin baya sunkuyawa wanin Allah, yayin da wanda yake sunkuyawa wanin Allah za ka same shi cikin azaba ta damuwa da rudewa, yana mai kasancewa baya tabbata akan hali guda, kuma ba yada yarda ta hakika da daya daga cikin wadannan da yake bautawa, ba wai dukan su ba!

Yana daga cikin ababen da manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) Ya kebanta da su:

Cewa Shi ne Ya zo da wannan Alkur'ni, wanda Ya kasance mu'ujiza dawwamamma har macha' Allah. Kuma Allah (madaukaki) Ya kalubalanci dukkan 'yan adam da su zo da kamar wannan Alkur' anin, wanda ya kunshi gaskiya da dalilai bayyanannu; tamkar imani da gaibu tare da tabbatar da hakan da hujjuji wadanda suka kai matuka wajen gamsarwa. Ya kuma kunshi husa'ar magana da tasiri a kan mai sauraren Shi dakuma ilimi, da sauran su.

Lalle Shi mu'ujiza ce wanzazza ta manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi).

Yana kuma daga cikin manya manyan ayukkan Shi ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) kasancewar ya isar da umarnin Allah madaukaki ba tare da ya boye ko rage wani abu ba, kuma Allah Ya kiyaye wannan addinin a hannun sahabban shi ( Allah Ya dada yarda da su ), har zuwa yau musulmi sun san addinin su cikekken sani, kamar yanda suka san tarihi da rayuwar manzon su ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) , kai har sun san abin da ya shafi shakalin Shi; sun san yawan hurhura da ke cikin gyeman Shi, sun san tsawan Shi da launin Shi, sun san irin tufafin da yake sanyawa, kuma me yake sakawa a kan Shi, kamar yanda suka san me Yake aikatawa a cikin gidan Shi harma tare da matan Shi, kuma me Ya ke aikatawa a waje, me yake aikatawa a masallaci, a cikin kasuwa, a halin yaki da halin kwancin hankali… kai dukkan rayuwar Shi ta kasance sananna ce, tare da dalilai wadanda ba sa barin wani shakku !

Wannan kwa sabanin tarihin sauran annabawa ne, domin mutane sun manta da yawa daga cikin ababen da suka kunshi rayuwarsu, sai ya kasance wadannan ababe kadan ne, kuma suma ba bu tabbas game da su, hasali ma wani sharen karya ne da aka lika masu; domin ba su cancanta ba ga annabawa, kuma yana tauye matsayin Su ! kamar ga misali: nuna cewa su mutane ne wadanda bangaren sha'awar su ya rinjaye Su, ko abinda ya yi kama da haka daga ababen da gama garin mutane na kirki ma ba su siffantuwa da shi, ba wai annabawa ba da Allah Ya zaba a cikin mutane; domin su isar da sakonnin Shi. Irin wannan labaru yahudawa da makamantan su ne su ka kirkiro su; domin su bata surorin annabawa wajen jama'a, amma manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) tarihin Shi bai gushe ba bayyananne ne a wajen musulmi.

 

Yana kuma daga cikin manya manyan ayukkan Shi: kasancewar Ya isar da wannan addinin isarwa wadda ta wadatar da dukkan duniya; domin manzoncin Shi Ya shafi dukkan mutane da aljannu ne, ba wai ya kyebanta da wasu jama'a ne, ko wani lokaci ba, wannan kuma har tashin duniya.

Yana kuma daga cikin manya manyan ayukkan Shi ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ): kasancewar Ya hada kan al ummah da tayi imani da Shi, Ya sanya su al ummah guda, tare da sabanin garuruwan su, da kabilun su, da launin fatar su; bakake ne su ko farare, larabawa ne ko farisawa… dukkan su sun kasance 'yan uwa masu son junan su, sharen su yana taimakawa share, mawadaci a cikin su yana taimakawa wanda ba shi da..

 

Shahararran malamin nan na tarihi dan Britaniya Arnoldtoynbee yana cewa a cikin littafin shi "Civilizatio on Trial" - yayin da yake bayani akan sababin gushewar al ummomin mutane da suka shude, kuma abin da yake kalubalantar yammacin duniya wanda yake kai su ga banbanci sa'annan yaki -: "dukkan wadannan al ummomi - wadanda suke sanannu wajen dukkan malaman tarihi na yammacin duniya – sun kau ne saboda yaki ko banbanci, ko kuma dalilen biyun a hade" sa'annan ya ci gaba da cewa: "..kawar da banbanci tsakanin mutane a cikin jama'ar musulmi ya kasance daya daga cikin manyan ayukka -da suka shafi halayya- da muslunci ya ba da kyakyawan misali, lalle kwa a cikin duniyar mu ta yau muna matukar bukatar anfana da wannan kyakyawar halayyar ta muslunci".

 

Da wannan al ummar guda ne muslunci ya tsaida daula tsararra, kuma wannan daular ta kasance a tsaye tana mai daga tutar wannan addinin, kuma tana kira zuwa gare shi, tare da yakar daulolin da ke hana mutane shiga addinin muslunci; domin mutane su kasance suna da incin karbar muslunci ko kuma kin karbar Shi.

Wadanda suka zabi rishin karbar muslunci daular muslunci tana neman wani kudi wanda bashi da yawa a wajen su; sakamakon kula da kiyayewa da kariya wacce daular muslunci zata ba su daga tsutarwar ta dukkan wani makiyi, ko kuma yayin da suka manyanta suka kai lokacin da ba za su iya kula da kanun su ba !

Lalle bayyanar muslunci ya kasance juyin juya hali mafi ban mamaki a tarihin 'yan adam; wannan juyi - da ya gudana a hannun manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) - yayi tasirin gaske a kan larabawa, sa'annan sauran al' ummomi, tasiri wanda ba' a taba ganin irinshi ba, tasiri mai ban mamaki ta ko wace huska: mai ban mamaki ta bangaren gaggawar watsuwar shi, ta bangaren fadi da zurfin shi a cikin zukata, ta bangaren kasancewar shi a bayyane da saukin fahinta; bai kasance abin da ba' a bayyane ba tamkar da yawa daga cikin ababen mamaki da suka wuce hankali.

 

Malamin tarihi doctar Mikal Hars a cikin littafin shi "sanin mutane dari na farko da suka yi tasiri ", shafi 19: ((zaben muhamad domin Ya kasance na farko cikin mutane dari cikin mutane da suka yi tasiri, zai iya ba masu karatu mamaki , abin da zai sasu tambayoyi masu yawa, amma a tunani na Muhamad ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) Shi kadai ne a tarihi da Ya ci nasara ta gaske kuma bayyananna a bangaren abin da ya shafi lahira da duniya ! lalle Muhamad ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) Ya gina, kuma Ya yada daya daga cikin mafi girman addinai a duniya, kuma Ya kasance daya da cikin manyan jagororin siyasa na duniya. Kuma a yanzu, bayan shudewar karni goma sha uku da mutuwar Shi, har yanzu tasirin Shi bai gushe ba yana mai karfi)).

Yana kuma daga cikin manya manyan ayukan Shi ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) : kasancewar shi ya gina al' ummah mai daukaka a cikin halayya, da tasiri a cikin rayuwa; lalle Ya kasance Yana tarbiyantar da zukatan su akan Alkura' ni, kuma Yana bunkasa imani a cikin zukatan su, suna ma su meka wuya gaban mahaliccin su, so biyar a yini, tare da tsarki na zuciya, da nitsuwa ta zuciya; da haka kulun suna kara tsarkake zukatan su, tare da yakar san ran su.

 

Yana kuma daga cikin manya manyan ayukan Shi ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) : kasancewar laraba sun samu karfi bayan sun karbi muslunci, alhali kwa sun kasance cikin rauni gabanin haka; sun dau nauyin sako mai girma wanda Shine muslunci; sai suka kasance suna masu yakar zalunci, masu yada adalci, al' ummah mai canza tsoron mai rauni da aminci, al' ummah da ke fafatakar 'ya'yan ta su jagoranci al' ummomi zuwa ga ga'bar tsira da imani!

Yana kuma daga cikin manya manyan ayukan Shi ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ):  kasancewar Shi Ya ci nasara game da yakar dukkan karkata a cikin rayuwar dan adam, karkata ta bangaren zamantakewa, da tattalin arziki, da addini; sai kuma Ya sanya wa mutane mizani na adalci wanda za' su koma gare shi, wanda Shine Alkur'ni da Allah ma daukaki Ya saukar gare Shi, da sunnar Shi ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi )  wadda aka ruwaito daga gare Shi ba tare da sakaci ba; dan haka shari'ar Shi ta kasance tana mai hani daga algush, da zalunci, da girman kai, da karya, da al' fasha, da yanke zumunta, da wanin wannan; wannan kuma shi ya sanya shari' ar muslunci ta hade dukkan rayuwa, kuma tana biyan bukatun dan adam na zamanin shi wadanda mahaliccin shi, shine Ya san su; domin Shine Ya san halittar Shi, Shi ne kuma mai tausayi, masanin kome.

Kuma yana daga cikin manya manyan ayukan Shi: kasancewar Shi ya zo da shari'a daga Ubangijin Shi, wacce kuma a cikin ta babu wani abu da yafi karfin dan adam, kuma mai kare masalahar shi, tare da samar da ababen da za su taimaka mishi wajen awaitar da ita ba tare da damuwa ba; yana mai son ta yayin da yake aikata ta.

Yana kuma daga cikin manya manyan ayukan Shi ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ): kasancewar Shi Ya zo da shari'a wacce ba ta banbanci tsakanin 'yan adam, mai daidaitawa tsakanin su, hasali ma ta sanya dukkan mutane daidai suke game da hukunce hukunce; sai adalci ya kasance sifa mafi muhimmanci a cikin muslunci.

Manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) Yana cewa: ((ya ku wadanda kuka yi imani: abinda ya halaka wadanda suka gabace ku shine: idan mai daukak a cikin su ya yi sata sai su bar shi, idan kwa mai rauni a cikin su ya yi sata sai su zartar da hukuncin haddi akan shi, ina rantsuwa da Allah, idan da Fatima 'yar  manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) za ta yi sata da Na yanke hannun ta)) bukhari da muslim suka ruwaito shi.

Yana kuma daga cikin manya manyan ayukan Shi ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ):  kasancewar Shi Ya zo da tafarki daga Ubangijin Shi, tafarki mai kama da junan shi, wanda babu wuce gona da iri a ciki; tafarki wanda ba ya azbtar da jiki dan ya daukakar da rai, kuma ba ya wofintar da rai dan jiki ya ji dadi, kamar yanda ba ya ta'kura dan adam dan masalahar jama'a ko kasa, tare da cewa ba ya sakewa dan adam da ragama ya biya bukatun shi marassa kyau yana mai cutawa rayuwar jama'a.

Yana kuma daga cikin manya manyan ayukan Shi ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ):  kasancewar Shi Ya bude kofa ta ci gaban 'yan adam a cikin al amurran shi na duniya, tamkar fusa'a da kere kere, da kimiya, da sauran ilimi na ci gaban duniya; hasali ma manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi )  Ya hore mu da mu kyautata aiki yayin da muka aikata shi, kai kuma fiye da haka; ya hore mu akan cewa: tare da kyautata ayukkan mu, kar mu manta da lahirar mu; domin ita ce mafi akhairi, tare da dawwama.

Kai ya isa abin alfahari gare Shi ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi )  kasancewar Shi bai danganawa kan Shi abin da bai cancance nashi ba; ya hana a yabe Shi da abinda ba hakanan ne ba; wani mutun ya ce da Shi: abinda kai da Allah kuka ga dama, sai Yayi fushi, ya ce: ka sanya ni kishiya ga Allah? A'a abinda Allah Shi kadai Yaga dama. Kuma Ya ce: kar ku wuce gona da iri wajen yabo na, Ni bawon Allah ne, kuma manzon Shi ne, ku ce: bawan Allah kuma manzon Shi ! da kissosi da su kayi kama da haka … wadanda ke nuna rishin giman kan Shi, da gudun duniyar Shi ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ).

Kuma Ya kasance Yana baiwa annabawan da suka gabace Shi matsayin su da daukakar su; kamar fadar Shi: (kar wanada yace Na fi yunus dan Matta); Yunus daya ne daga cikin annabawa (tsira da amincin Allah su tabbata a gare su), ya hana a fifita Shi akan Shi, fifitawa ta reni; domin kamar yanda ya zo a cikin alkura'ni Allah Ya fifita wasu annabawa akan wasu, tare da cewa dukkan su sunada matsayi mai girma wajen ubangijin su, amma darajar su ta sha banban duk da cewa dukkan su annabawa ne, Allah Ya zabe su.

Wanda ke fifici tsakanin annabawa da nifin kaskantar da wani daga cikin su, ko danganta wata nakasa gare Shi, to lalle ya aikata babban laifi; gaskiya ita ce: dukkan su annabawa ne, zababbu ne wajen Ubangiji, duk da cewa manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) shine fiyayyen su, kuma wasu daga cikin sun fi wasu, amma ba tare da kaskantar da wasu ba.