alkur'ani maganar Allah madaukaki ne


alkur'ani maganar Allah madaukaki ne

 

musulmi suna da imanin cewa alkur'ani maganar Allah ne, suna ganin cewa su basu ba alkur'ani hakkin Shi da ya kamata ba – dudda kokarin da suke game da Shi – ta bangaren sifanta Shi da sifar da ta yi daidai da Shi. Wannan kwa saboda tasirin da alkur'ani yake yi a cikin rayuwar su ta yau da kullun, da kuma ababen da suke kara bayyana gare su wadanda ke goda cewa shi alkur'ani yana daidai da ko wane guri kamar yanda yake daidai da ko wane lokaci.

 

Mi ya sa musulmi suke ga cewa alkur'ani maganar Allah ne ?

Lalle suna imani da cewa alkur'ani shine mafi girmar muajiza da Allah ya baiwa manzon Shi muhamad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ).

Muhamad mutun ne wanda bai san rubutu ko karatu ba, kaka ya zo da wannan littafin mai girma, da buwaya ?

Mai karanta Alkur' ani zai yi mamakin  maudu' o' in shi wadanda suke masu caccanzawa:

Mamakin yanda yake zuwa da kissosi tare da caccanza uslubi.

-Mamakin yanda yake sifanta kyawon kauni da abin da ya kunsa na da ga sammai da kassai da abin da ke cikin su na khalittu, da abin da ke cikin teku da sauransu.

-Mamakin yanda yake sifanta jikin mutun da abin da ya kunsa, da matakai na rayuwar shi tun daga kasancewar shi a cikin ciki har zuwa tsufan shi.

-Mamakin yanda yake sifanta rai da da abin da ta kunsa …

Yana bada mamaki da kayatarwa ta bangarori masu yawa da ba ka samu tare da wanin shi.

Shin wani balarabe duk yanda wayon shi ya kai zai iya kirkiro wannan Alkur' anin ?

Shin zai yuwu a ce balarabe dake rayuwa a cikin sahara, ya na kiwon dabbobi tsakanin duwatsu, wanda ke rayuwa a Makkah, wanda bai taba barin Makkah ba banda so biyu da ya tafi sham:

- tafiya ta farko tare da kawun shi abu talib, wannan kwa kafin ya balaga, bai kuma rabu da shi ba cikin wannan tafiyar.

- tafiya ta biyu tare da Maisara tafiya ta kasuwanci yana da shekaru ishirin da 'yan kai, sun kuma kasance tare da mutane da suka san halin shi a cikin wannan tafiyar. Bai taba haduwa ba da wani masani na yahudu ko nasara ko waninsu ba, amma Buhaira malami na nasara da ya gan shi ya gane Shi saboda ya karanta sifofin shi a cikin litattafen su, sai ya sanarda mutanen shi cewa su kula da shi kar yahudawa su cutar da shi.

Bai taba karatu ba wajen wani ba; dan haka Allah yake kare shi a cikin Alkura' ni daga zargin wadanda ke tuhumar shi da cewa ya dauko shi ne daga wani mutun.

Allah ya ce: « Kuma lalle ne, haƙĩƙa Munã sanin ( cẽwa ) lalle ne sũ, sunã cẽwa, Abin sani kawai wani mutum ne yake karantar da shi. Harshen wanda suke karkatai da maganar zuwa gare shi, Ba'ajame ne, kuma wannan ( Alƙur'ãni ) harshe ne Balãrabe bayyananne ». [ suratun –nahl 103 ].

A cikin wannan aya Allah ya musu raddi; saboda kaka zai samo wannan alkura' ni daga yahudu ko nasara kuma ya kasance da larabci su ko ba larabawa ba ne ba ?!

Kaka mutun mai tarihi kamar haka zai iya zuwa da littafi mai kama haka ?!!

Inda Shi ya kirkiro Shi ne da zai kunshi rayuwar larabawa ne a cikin sahar,  da abin da ya dami larabawa a wannan lokati; rakumi, dawaki, dabbobi, kabilun larabawa, da abin da ke damun su kamar karamcin ruwa, ko matsalolin talauci…

Sai dai mai karanta al kura' ni zai ga cewa Wannan littafin mu' ajiza ne ta bangaren fasaha da bayani da ke cikin shi, ta bangaren cewa ya shafi dukkan bangarori na rayuwa; yana shiryarwa ga hanya mikakka, yana tsara rayuwar mutun tare da la' akari da matsayin shi na kasancewa daya daga cikin jam'ar shi, ya na cike da karantarwa game da abin da ya shafi siyasa da tattalin arziki, , ya na cike da ilimi na likita da yanayi da tarihi …

Yana kuma gabatar da wannan ababe ne ta hanya mai kayatarwar gaske, wadda bata da wahalar fahinta ko kadan !!

Shari' ar shi kwa tana dacewa da ko wane lokaci kamar yanda take dacewa da ko wane guri; tana dacewa da rayuwa duk inda ta kai a ci gaba.

Duk wannan ba tare da sharen Shi yana warware share ba, babu tubka da warwara ko da a guri guda daya !!

Abin mamaki wannan ko ya kasance sifa ta al kura' ni tare da cewa an saukar da Shi ne a cikin shekaru ishrin da uku, yana mai sauka dai dai da ababen da suke abkuwa a cikin rayuwar mutane a wancan lokaci, inda muhamad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ne ya kirkiro shi, da sai ya karanta musu shi a lokaci guda, ya kasance kuma mai maimaita musu karatun shi!

Za' ka kuma kara mamaki idan ka ga kalubale da al kura' ni ya yi ga kuraishawa da ma dukan mutane, wannan kwa a ko wane lokaci, na su zo da kamar wannan al kura' nin, ko kuma su zo ko da kamar sura guda daya, abin da suka kasa har yanzu, kuma ba za su iya ba har abada.

Wannan kuma kalubale ne ga dukkan mutane har tashin duniya.

 

Allah ya na cewa: « Ka ce: Lalle ne idan mutãne da aljannu sun tãru a kan su zo da misãlin wannan Alƙur'ãni bã zã su zo da misãlinsa ba, kuma kõ dã sãshinsu yã kasance mataimaki ga sãshi ». [ Suratul Al-isra' a 88].

Lalle son alkura' ni da imani da shi da tasirantuwa da shi bai takaitu da lokacin da manzo ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) yake ra'ye ba; al ummomi daban daban –larabawa da wadanda ba larabawa ba- sun ci gaba da rungumar Shi da kuma imani da Shi.

Shin littafi wanda mutun ya wallafa zai iya samun wannan karbuwa ba tare da yankewa ba, kuma daga al ummomi daban daban ?

Lalle dalilai ma su yawa suna tabbatar da cewa Shi Alkura' ni maganar Allah ne, ba wallafar manzo muhamad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ba ne ba.

 

Ga kuma Karin dalilai a kan hakan:

1- da Shi alkura' ni daga manzo muhamad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) kaka za' a samu ayoyi a cikin Shi wadanda ke kunshe da tsoratarwa gare Shi idan ya fadi wani abu wanda ba Allah ya fada ba ?

 

Allah ya na cewa: « Kuma dã ( Muhammadu ) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu. 
Dã Mun kãma shi da dãma. 
sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã. 
Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre ( azãbarMu ) daga gare shi ». [Suratul Al-Haqqah 44-47].

Yana kuma cewa: « Kuma kamar wancan ne Muka saukar da shi, Hukunci a cikin Lãrabci. Kuma lalle ne idan kã bi son zuciyõyinsu a bãyan abin da ya zo maka na ilmi, bãbu wani masõyi a gare ka mai kãre ka daga Allah, kuma bãbu matsari ». [Suratul Al-Ra'd 37].

 

Da a ce daga muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ne, shin zai bar irin wadannan ayoyi ?

Kayi tunani a game da wannan kashen da a kayi wa manzo ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi )

« Kuma lalle ne sun yi kusa haƙĩƙa, su fitinẽ ka daga abin da Muka yi wahayi zuwa gare ka, dõmin ka ƙirƙira waninsa a gare Mu, a lõkacin, haƙĩƙa, dã sun riƙe ka masoyi. 
Kuma bã dõmin Mun tabbatar da kai ba, lalle ne, haƙĩƙa, dã kã yi kusa ka karkata zuwa gare su ta wani abu kaɗan.          
A lõkacin, lalle ne, dã Mun ɗanɗana maka ninkin azãbar rãyuwa da ninkin azãbar mutuwa, sa'an nan kuma bã zã ka sãmi mataimaki ba a kanMu ».

Hasali ma wasu ayoyi sun zo suna masu gargadi ga Muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) daga kasawa wajen isar da sako ga al – ummah.

Allah yana cewa a cikin Alkura' ni: « Yã kai Manzo! Ka isar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka. Kuma idan ba ka aikata ba, to, ba ka iyar da manzancinSa ba ke nan. Kuma Allah Yanã tsare ka daga mutãne. Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai ». [ Suratul Al-Ma'idah67].

Shin da daga Muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi )  ne zai bar irin wadannan ayoyi ?

Inda daga Muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ne kaka zai bar ayoyi da ke  da koy kashe gare Shi a cikinsu ?

Allah yana cewa a cikin Alkura' ni: « Yã game huska  kuma ya jũya bãya. 
Sabõda makãho yã je masa. 
To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka. 
Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi? ». [ Suratul Al-isra 73-75].

Haka ma alkura' ni ya yi bayanin abin da manzo ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ya boye a cikin zuciyar Shi game da auran Shi da zainab 'yar jahsh ( Allah ya kara yarda da ita ).

Allah yana cewa a cikin Alkura' ni mai  girma: « Kuma a lõkacin  da kake cẽwa ga wanda Allah Ya yi ni'ima a gare shi kai kuma ka yi ni'ima a gare shi, Ka riƙe mãtarka, kuma ka bi Allah da taƙawa, kuma kana ɓõyẽwa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana shi, kanã tsõron mutãne, alhãli kuwa Allah ne Mafi cancantar ka ji tsõronSa. to a lõkacin da zaidu ya ƙãre bukãtarsa daga gare ta, Mun aurar da kai ita, dõmin kada wani ƙunci ya kasance a kan mũminai a cikin ( auren mãtan ) ɗiyan hankãkarsu, idan sun ƙãre bukãta daga gare su. Kuma umurnin Allah yã kasance abin aikatãwa ».

Kuma yanda Alkura' ni ya yi bayani a fili game da matsayin manzon Allah ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) na cewa Shi mutun ne mai isar da sakon Allah ga mutane, kuma bai mallaki cutarwa ko anfanarwa ga mutane ba, kuma ba ya neman wani sakamako a kan isar da wannan sakamako face gun Ubangijin Shi. Wannan hakika dalili mai karfi da ke tabbatar da cewa Shi alkura' ni daga Allah ya ke ba daga Muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ba.

Ka yi tunani game da:

1 – bayanin alkura' ni a kan matsayin manzon Allah ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) da bayanin tabbatar da cewa Shi lalle mutun ne wanda a ka fifita da wahayi:

Allah ya na cewa: « Ka ce: Ba zan ce muku, a wurina akwai taskõkin Allah ba. Kuma ba ni sanin gaibi, kuma ba ni gaya muku cẽwa ni malã'ika ne. Ba ni bi, fãce abin da ake yiwo wahayi zuwa gare ni.   Ka ce:  Shin, makãho da mai gani sunã daidaita? Shin fa, ba ku yin tunãni? ». [Suratul Al-An'am 50].

Yana kuma cewa: « Ka ce: Bã ni mallaka wa raina wani amfãni, kuma haka ban tunkuɗe wata cũta, fãceabin da Allah Ya so. Kuma dã na kasance inã sanin gaibi, dã lalle ne, nã yawaita daga alhẽri kuma cũta bã zã ta shãfe ni ba, nĩ ban zama ba fĩce mai gargaɗi, kumamai bãyar da bishãra ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni ». [Suratul Al-A'raf 188].

« Ka ce: Yã kũ mutãne! Lalle ne nĩ manzon Allah nezuwa gare ku, gabã ɗaya. ( Allah ) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni daAllah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa ». [Suratul Al-A'raf 156].

Ka ce: « Yã kũ mutãne! Idan kun kasance a cikin kõkanto daga addinĩna, to bã ni bauta wa,waɗanda kuke, bautã wa, baicin Allah, kuma amma ina bauta wa Allah wanda Yake karɓar rãyukanku. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu ĩmãni ». [Suratul Yunus 104].

2-  umarnin Alkura' ni ga manzon Allah ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) da ya yi biyayya ga abin da aka saukar mi Shi:

Allah ya na cewa: «Kuma ka bi abin da ake yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ka yi haƙuri har Allah Ya yi hukunci. Kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci ». [Suratul Yunus 109].

Allah ya na kuma cewa: « Sa'an nan Muka sanya ka a kan wata sharĩ'a ta al'amarin.Sai ka bĩ ta, Kuma kada kã bi son zũciyõyin waɗannan daba su sani ba  » . [ Suratul Al-Jathiya 18].

3- umarnin Alkura' ni gare Shi a kan ya bi abin da a ka saukar gare Shi na wahayi, wanda kuma yak e kiran mutane zuwa gare Shi:

Allah ya na cewa: «Sai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kai da waɗanda suka tũba tãre da kai kunã bã mãsu ƙẽtara haddi ba. Lalle shĩ, Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa» .  [Suratul Hud 112]

Allah ya na kuma cewa:  « Sabõda haka, sai ka yi kira kuma kai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kuma kada ka bi son zũciyõyinsu, kumaka ce, Nã yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar na littãfi, kuma an umurce ni da in yi ãdalci a tsakãninku. Allah ne Ubangijinmu, kuma Shĩ ne Ubangijinku, ayyukanmu nã gare mu, kuma ayyukanku nã gare ku, kuma bãbu wata hujja a tsakãninmu da tsakãninku. Allah zai tara mu, kuma zuwa gare Shi makõma take ». [Suratul Al-Shura 15].

4- kasancewar Alkura' ni ya na tsoratar da Shi game da sabawa umarnin Allah:

Ka ce: « Shin, wanin Allah nike riƙo majiɓinci, ( alhãli Allah ne ) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa, kuma Shi, Yanã ciyarwa, kuma ba a ciyar da Shi? Ka ce: Lalle ne nĩ, an umurce ni da in kasance farkon wanda ya sallama, kuma kada lalle ku kasance daga mãsu shirki. 
Kace: Lalle ne nĩ inã tsõron azãbar Yini Mai girma, idan nã sãɓã wa Ubangijina ». [Suratul Al-An'am 14- 15].

5 – Alkura' ni ya na umarnin Shi da ya kasance tare da muminai, kuma yayi hakuri a kan hakan:

« Ka haƙurtar da ranka tãre da waɗanda ke kiran Ubangijinsu, sãfe da maraice, sunã nufin yardarSa. Kuma kada idãnunka su jũya daga barinsu, kanã nufin ƙawar rãyuwar dũniya. Kuma kada ka biwanda Muka shagaltar da zũciyarsa daga hukuncinMu, kuma ya bi son zuciyarsa, alhãli kuwa al'amarinsa ya kasance yin ɓarna ». [Suratul Al-Kahf 28].

Lalle irin wadannan umarni  ga manzon Allah ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) suna tabbatar da cewa shi wannan Alkura' ni maganar Allah ne, ba wani abu neb a wanda Muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ya kirkiro.

Kamar yanda wasu hujjoji na hankali da kyere kyere na zamani suka zo da su suna tabbatar da cewa Shi Alkura' ni maganar Allah ne.

"mutun yana  Magana a kan abin da ke kewaye da shi ne a lokacin shi, dan haka za ka same shi yana koro akidu ko ababen da suke na ilimi dake a cikin zamanin shi, wannan ko shine ya sa za ka ga dukkan littafi da aka wallafa, bayan wani lokaci kurakurai ma su yawa suna bayyana a cikin shi sakamakon ci gaban ilimi.

Amma Alkura' ni ba haka ne ba, ko wane zamani ya na dada tabbatar da cewa shi maganar Allah ne, wanda yayi kewayo da kome da kowa.

Shi gaskiya ne a cikin dukkan ababen da ya fada fiye da karni goma sha fudu, tare da cewa babu wani sauyi da ya abku a cikin Shi. Wannan ko babban dalili ne da ke cewa shi maganar Allah - mahaliccin dukkan abin halita - ne, wanda ya san halin kome a ko wane lokaci a ko wane guri.

Inda Shi Alkura' ni maganar mutun ne da lokaci ya karyatar da shi, domin zai zo da ababen da suka saba ma wancen zamanin.

Lalle ababe da yawa wadanda na farko sukayi bayani a kan wasu daga bangarori su, yau ilimi na zamani ya na tabbatar mana cewa masaniyar su takitatta ce game da wadannan ababe.

Ya na daga cikin kasancewa Alkura' ni mua'jiza ne kasancewar Shi yana magana da harshen ilimi ne wanda ko na farko ma suke fahintar ma'anar shi, tare da cewa wannan harshen ya kunshi dukkan abin da ilimi na zamani ya zo da shi.

Ga wasu daga cikin misalai:

Allah madaukaki ya na cewa a cikin Alkura' ni mai tsarki: « Allah Shi ne wanda Ya ɗaukaka sammai, bã da ginshiƙai ba waɗanda kuke ganin su… ». [ Suratul Al-Ra'd 2 ].

Wannan ayar ta yi daidai da yanda mutun yake ganin sammai a can baya; saboda ya na ga abin halitta babba wanda ke tsaye ba da wani ginshiki ba, wanda kuma ya kunshi rana da wata da tauraru, yayin da shi ma mutun na wannan zamanin yake samun tafsiri ga abin da yake gani wanda ke cewa sammai bas u da ginshikai masu rike su, duk da cewa a kwa wasu ginshikai wadanda ba' a ganin su, tare da cewa suna rike wannan saman; sune ginshikan karfi na jayeyyeniya tsakanin dukkan ababen halitta wanda ilimi ya gano, shi kwa wannan karfi shi ne yake sa kome ya tsaya a gurin shi da ikon Allah.

A- ya zo a cikin Alkura' ni game da rana da tauraru: « Rãnã bã ya kamãta a gare ta, ta riski watã. Kuma dare bã ya kamãta a gare shi ya zama mai tsẽre wa yini, kuma dukansua cikin sarari guda suke yin iyo ».

Mutun a lokacin da ya gabata yana ga tauraru suna motsi, suna masu canza guri daga wani lokaci zuwa wani lokaci. Dan haka ba su samu wannan  uslubin maganar ta Alkura' ni abin mamaki ba, haka kuma ilimi na zamani ya tabbatar da cewa babu wata kalima da za' a sifanta halayan wadannan ababen halitta warda tafi kalimar "iyo" saboda juyawar da suke a cikin wani fili mai fadin gaske.

C - ya zo a cikin Alkura' ni game da dare da rana: «  Lalle ne Ubangijinku Allah ne, wanda Ya halitta sammai da ƙasa a cikin kwãnaki shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, Yanã sanya dare ya rufa yini, yanã nẽman sa da gaggawa, kuma rãnã da watã da taurãri hõrarru ne da umurninSa ». [ Suratul Al-A'raf 54 ].

Wannan ayar ta nunawa mutun na wancan lokaci kaka ne dare ya ke zuwa bayan rana, kamar yanda ta kunshi nuni ga juyawar kasa wanda ke masabbabin caccanzawar dare da rana, wannan ko shi ne abin da ilimi ya ke tabbatarwa.

Ya na daga cikin kasancewa Alkura' ni mua'jiza ne  abin da ya zo a cikin Alkura' ni: « Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa ». [ Sũratul kiyãma 4 ].

Saboda me a ka kebe gaɓõɓin yãtsu da anbato ? me ke tare da su ?

Wannan mu'ujizar Ubangiji ce; dukkan mutun ya na da zane na gabban yatsotsu wadanda ba su yi kama da kowa ba!!

Wannan abin mamaki ne wanda ilimi bai gano ba inba nan kusa ba. Babu wani wanda ya san da haka a zamanin Muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ko zamanin da ya biyo baya.

Lalle wannan muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ya karbo shi ne da ga Ubangijin Shi, lalle kuma wannan ya na cikin ababen da ke nuni cewa Shi Alkura' ni maganar Allah ne. haka ma a cikin Alkura' ni a kwai ire iran wadannan ma su yawa, wadanda lokaci zuwa lokaci a ke ganowa, saboda mu'ujizojin Shi ba su karewa.

Saboda tabbatar da abin da ya gabata na cewa musulmi ba su yi kewayo ba ga muajizojin Alkura' ni ba, abin da ke da koy shi ne sun san wani abu da ga ciki, zan tafi da ku zuwa wani nau' i daban:

1 – abin da Alkura' ni ya ke bada labari a kai na da ga ababen da za su abku a gaba, ga abubuwa biyu da ga cikin su:

A – Alkura' ni ya bada labari a kan cewa kawun manzon Allah( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi) Abu lahab zai mutu ba tare da ya yi imani ba, abin da ya kuma abku, tare da cewa shi abu lahab ya ji wannan ayar, amma ko dan ya karyatar da Alkura' ni bai ce ya yi imani ba, ko da a baki !!

B – labari da Alkura' ni ya bada game da cewa mutanen rum za su samu nasara a kan farisa, bayan farisawa sun ci su da yaki.

Wannan ko ya abku kamar yanda Alkura' ni ya fada.

2- ababen da ya kasance ya na mai bada labari a kan su na da ga labarun al ummomi da suka gabata musamman a lokacin zaman manzon Allah a Madina.

Alkua' ni ya kasance ya na mai raddi ga yahudawa wadanda suke Madina game da ayoyin da suka caccanza; kamar da' awar da suke ta cewa Isa an tsire Shi ne, da fadar wasu da ga cikin su cewa Shi dan Allah ne, da fadar wani shashen su cewa Shi mai sihiri ne, haka ma sukar su ga Annabi sulaiman da cewa Shi mai sihiri ne.

Haka ma Alkura' ni ya na ba da labaren Annabawa da suka gabata ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare su gaba daya) tare da cewa yahudawa suna sauraren Alkura' ni da abin da ya ke labarantarwa game da manzon Allah Musa ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ), amma duk da haka ba' a taba samun wani da ga cikin su ya karyata Alkura' ni ba !

Ya na daga cikin mu'ujizar Alkura' ni kasancewar maganganun da ke cikin Shi ba su warware junan su, inda ko daga wanin Allah ne da an samu sabani mai yawa a cikin Shi.

Allah ma daukaki ya na cewa: « Shin, bã su kula da Alƙur'ãni, kuma dã yã kasance daga wurin wanin Allah haƙĩƙa, dã sun sãmu, a cikinsa, sãɓã wa jũna mai yawa ». [Suratul Al-Nisa 82].

4- Allah ya dau nauyin tsare Shi da ga dukkan canji ko sauyi, wannan kwa shine abin damu ke gani a yau; dukkan musulmi ba su da face Alkura' ni guda, a ko ina ko suke! A shina, kwa america, ko india …

5 – saukin hardar Shi har ga wa 'ynda ke ba su san kalima guda ba a cikin harshen larabci !

Ya kai dan uwa mai neman gaskiya:

Lalle ta'sirin Alkura' ni game da jawo hankullan larabawa zuwa gare Shi babba ne, su ne ko wadanda su ka shahara da iya magana da bayani, ba kuma kwa wace magana ba ce za ta ja'  hankullansu ba, kai har ma Alkura' ni ya kasance mai jawo hankullan su ga ma' anonin Shi da karantar Shi, ba wai kalimomin shi ba kadai.

Wannan kwa a lokacin da adawa ga manzon Allah da da'awar musulunci tayi kamari, wannan kuma ya bamu wani sabon yanayi na karfin Alkura' ni da kasancewar Shi mu' ajiza !

Kissar shugabanin kuraish guda ukkunnan babban dalili ne a kan haka; su ne kwa: Abu sufyan dan Harb, da abu jahl dan Hisham, da ahnas dan sharik.

Ko wane daya da ga cikin su ya ji dadin Alkura' ni kuma ya shiga zuciar shi, dan haka ko wane daya da ga cikin su ya ke bwoyewa da dare dan ya je ya saurari karatun Alkura' nin ba tare da wani ya gan shi ba, saboda dukkan su suna cikin manyan ma su adawa da manzon Allah ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ). Kaka halin shi zai kasance idan mutane suka san cewa ya na zuwa sauraren karatun Alkura' ni ?!

Ko wane daya da ga cikin su ya na zuwa da dare dan ya saurari karatun Alkura' ni lokcin da Muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi )  ya ke karanta Shi a cikin sallah, wannan ko ko wane daya da ga cikin su bai san da dan uwan shi ba, har sai lokacin da al- fijr ya gabato sai su hadu a kan hanya.

Sa' an nan su dau ma juna alkawalin cewa ba za su kara ba, domin idan mutane su ka sani abin ba zai musu kwau ba.

Al amarin bai tsaya nan ba, sun tsi gaba da zuwa, kamar yanda suka ci gaba da haduwa, bayan alkawurra ma su yawa … sabo da karfin ta' asirin Alkura' ni.

Abu ya kai inda ahnas dan sharik ya tambayi Abu jahl game da abin da ya ji na cikin Alkura' ni, sai Abu jahl ya ce da shi: "mu da kabilar muhammad ( banu abdi manaf ) mun kasance muna kunnan doki da su a wajen daukaka; sun ciyar mun ciyar, sun bayar mun bayar … har lokacin da muka daidaita sai suka ce: ana mana wahyi (aike da ga Allah ) wallahi ba za mu yi imani da shi ba har abada".

Yayin da adadin musulmi ya fara yawa, kafirai sun umarci daya da ga cikin su ya je wajen Muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ya ce masa: idan dukiya yake so, ko mulki, ko mata, za su bashi a kan ya bar wannan abin da ya zo da shi.

Wanda suka aika wajen manzon Allah ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) shine Utba dan Rabi' a, ya kuma isar da sakon su.

Amma ga amsar da manzon Allah ya bashi, bayan ya tambaye shi: "shin ka gama maganar ka ya utba ? ya kuma ba shi amser: na' am: "ka saurare Ni, sai ya karanta wani abu daga Alkura' ni, wanda utba ya tsaya ya na mai saurare, da maida hankali, har sai da ya gama, sa' an nan ya ce da shi: ka ji ya Utba ? abin da ya yi saura ya na wajen ka.

Sa' an nan ya tashi zuwa wajen mutanen da suka aiko shi, yayin da suka gan shi sai suka ce: wallahi utba ya dawo da huska ba wadda ya tafi da ita ba.

Alkura' ni ya yi tasiri a kan shi kamar yanda yake bayyana a cikin amser shi wadda take kamar haka: " lalle na ji magana wadda ban taba jin irinta ba, wallahi ba waka ba ne ba, ba kuma sihiri ba ne ko bokanci ba, ya ku mutanen kuraish ku dau abin da zan gaya muku, ku rabu da wannan mutun, wallahi wannan maganar da na ji zata kasance mai sha' anin gaske; idan larabawa sun samu nasara a kan shi, sun wadatar da ku daga tsutar da Shi, idan kuma ya samu nasara a kan su mulkin Shi mulkin ku ne, daukakar Shi daukakar ku ne, za ku fi kowa jin dadi ".

Sai su ka ce: wallahi ya sihirce ka da harshen Shi ya Utba ! sai ya ce da su: wannan shi ne ra'ayi na, sai ku aikata abin da ku ka gani.

Zan takaita a kan wadannan ababen biyu game da karfin ta'sirin Alkura' ni dake tabbatar da cewa Shi maganar Allah ne.

Alkura' ni mu'ujiza ne a bayyane ta fuskoki ma su yawa kamar yanda muka yi bayanin wasu daga cikin su: Shi mua'jiza ne ta bangaren lafazin Shi, da tsarin Shi, da sanya kalimomi ga ma'anoni wadanda su kayi daidai da su tare da balaga da iya magana …

ta bangaren bada labari game da sifofin Allah da sunayen Shi, da Mala'ikun Shi, da abin da yayi kama da haka …

ta bangaren bada labari a kan abin da ya gabata da abin da zai zo a gaba …

ta bangren bada labari game da makomar halittu gaba daya ….

ta bangaren bada dalilai na yakini da ma'aunai na hankali a cikin misalai wadanda ya ambata, kamar yanda Allah ya ke cewa: « Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun caccanza dõmin mutãne, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane misãli sai mafi yawan mutãne suka ƙi ( kõme ) fãce kãfirci ».  [ Suratul Al-Asra 89 ].

Mu'ujizar Alkura' ni wadda ta fi ko wacce girma ta na cikin shari'ar da ya zo da ita, wadda ke hadadda ba ta bar kome ba, mai tanadin rayuwar kyakyawa wadda dukkan mutun ya ke nema a ban kasa, wannan kuma shi ne sirrin da ya sa mutane ke son Shi, kuma su ke karbar Shi da hannu biyu biyu. Kuma saboda imanin su da cewa Shi maganar Allah ne wanda ya san abin da yake daidai da ko wane zamani kuma da ko wane lokaci, dan haka shari'ar muslunci ita ce ta kunshi ababen da ke gyara rayuwar dan Adam anan duniya da gobe kiyama.

Wadannan ababe da muslumci ya kebanta da su, da imani da cewa muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) manzon Allah ne, da kuma cewa Alkura' ni maganar Allah ne wanda ya sabkar ga Muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ), su su ka sa mutane suke dada karbar muslumci kamar yanda mu ke gani a yau. Kuma kullun karuwa su ke yi, dan rahama da adalci da sauki da suke gani a cikin wannan shari' ar, da ta'sirin Alkura' ni ga rayuwar wadanda su ka yi imani da muslumci.

Babban abin da ya fi dukkan ababen da suka gabata shi ne abin da a ka saukar da Alkura' ni dan shi; shi ne shiryar da mutane zuwa ga bautar Allah shi kadai, ba tare da hada Shi da wani ba a cikin bauta.

Shi ne mahalicci, mai mulki, mai juyar da al – amurra kamar yanda yake so; dan haka ne ya aiko manzanni, ya kuma saukar da litattafai ga wannaan manzannin.

Allah ya na cewa a cikin Alkura' ni mai guirma: « Yã kũ mutãne! Haƙĩƙa, Manzo yã je muku da gaskiya daga Ubangijinku. Sabõda haka ku yi ĩmãni yã fi zama alhẽri a gare ku. Kuma idan kun kãfirta, to, Allah Yanã da abin da ke cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima ». [ Suratul Al-Nisa 170 ].

Allah ya kuma ce a cikin Alkura' ni mai tsarki: « Kuma inã karanta Alƙur'ãni. To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai. Kuma wanda ya ɓãce, to, ka ce: Ni daga mãsu gargaɗi kawai nake ». [ Suratul Al-Naml 92 ].

 

Ma rubuci : mut'ab al- harisi