Daga cikin dalilen annabcin  Muhammad


 

Da sunan Allah mai rahama, mai jin kai

 

Daga cikin dalilen annabcin  Muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi )

 

Lalle wanda ya ke karantar tarihin mazon Allah  Muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) zai samu ababen da ke gaskatar da annabcin Shi; wannan ko ta huskoki hudu kamar haka:

1- tarihin Shi ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) da ya sha banban da tarihin dukkan wani abin halita, wannan tarihin kwa a cikin dukkan rayuwar Shi.

Lalle mun san manzon mu ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) da halayen Shi kyawawa, ya kuma shahara da gaskiya, da amana – har ya kai inda mutanen makkah sun kasance suna ma su bashi amana a kan mafi tsadar abin da su ka mallaka.

Khadija ( yardar Allah ta tabbata a gareta ) ta ma wakiltar da Shi a kan  kula da dukiarta ta kasuwanci gaba daya dan saboda tsananin amincewa da Shi, da son da mutane suke miShi.

Hakika ya shahara wajen mutane da hankali tare da adalci, dan haka Shi ne mutunan da mtanan Makkah suka hadu a kan yarda da ra'ayin Shi lokacin da kabilun kuraishawa sukasamu  sabani game da wace kabila ce za ta dora hajarul aswad a bagiren Shi; yayin da suke sake gina ka'aba.

A wannan lokaci ra'ayin Shi ya kasance magani ga wannan fitina da ta kusa abkuwa tsakanin su.

Dukkan ma su tarihi sun hadu a kan cewa ba'a taba samun wani wanda yake zargin Shi da karya ko cin amana ko hauka ba, ko da ko makiyin Shi ne. hasali ma hada su da yayi a kan dutsin safa yana nuna yarda da suka yi da hankalin Shi, da matsayin Shi da shaharar Shi da gaskiya a wajen su.

A lokacin ya ce da su: shin da zan ce mu ku:  ga wasu dawaki nan suna son su kawo muku hari, shin za ku gaskatarda Ni ? sai gaba dayan su suka bada amsar suna masu daga murya: sosai zamu gaskatarda kai, domin bamu taba saninka da karya ba !!

Rayuwar Shi kwa bayan annabci babban dalili ne a kan matsayin Shi da daukakar Shi ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ); ya rayu ya na mai dabi'u kyawawa mutuka, dan haka sai sahabban Shi suka so Shi fiye da dukkan wani abu, suka kuma fansar da rayun su da dukkan wani abu da suka mallaka wajen kare Shi. Kuma ya rayu rayuwa mai sauki, tare da gudun duniya.

Ababen nan suna nuni  ga cewa Shi mutun ne wanda tarihi bai samu kamar Shi ba, kuma ba zai samu ba, dan haka dukkan wanda ya san Shi ya na samun lamincewa da Shi, sa'an nan zai yi imani da cewa lalle Shi manzo ne daga Allah mai girma.

2 – abu na biyu: manufar Shi a cikin kiran Shi zuwa ga Allah, manufa ce wadda ta bayyana cewa mai kyawo ce da daukaka tun lokuttan farko na wannan da'awar. Mutanen Shi sun bijiro miShi da dukiya, kamar yanda suka bijiro miShi da mulki ko aurar daShi da mafi kyawo daga matan su, ya ki dukkan ababen da suka gabata, ya kuma bayyana musu cewa Shi fa manufar Shi ita ce: isar da sakon Allah zuwa ga kowa da kowa. Kuma rayuwar Shi ta yau da kullun ta tabbatar da cewa wannan ita ce manufar Shi.

Halayen Shi ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ya tabbata cewa  sun kai matuka wajen kyawo, dan haka mua'malar Shi da mutane ta kasance mai kyawo, yana mai afuwa ba tare da ya kasa ba, wannan kwa kafin addini ya samu rinjaye haka ma bayan ya same shi. Dan haka Shi bai kasance mai son mulki ko wata daukaka ba, abin da yake so shine shiriyar da bayi zuwa Allah ma daukaki.

Adiyu dan Hatim – wani dake kan addinin nasara – ya tasirantu da kyawon mu'amalar manzo( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ), wannan kwo a haduwar su ta farko.

Adiyu ya ce: sai ya tafi da ni zuwa gidan Shi, a hanya sai muka hadu da wata tsofuwar mace, sai ta tsayar da Shi, sai ya tsaya tare da ita lokaci mai tsawo tana gaya miShi bukatun ta, sai Adiyu ya ce: wallahi wannan ba mai son sarauta ba ne ba !

Sa'annan tarihi ba zai taba manta matsayin Shi game da wadanda suka tsutar da Shi  da sahabben Shi a Makkah, suka karyatarda Shi, suka nemi kashe Shi, hasali ma suka kashe da yawa cikin sahabben Shi, suka kuma kore Shi zuwa Madina, bayan dukkan wadannan ababe da suka gabata yayin da ya bude Makkah ya  tausaya musu, ya kuma musu mua'mala mai kyau; yayin da ya ce da su: me ku ke tsammani zan yi muku ? sai suka ce: ai kai dan uwa ne mai karamci, kuma dan dan uwa ne mai karamci. Sai ya ce da su: ku tafi ku duka intattu ne, ya musu afuwa !

3 – abu na ukku: shi ne dubi zuwa ga abin da manzon Allah ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ya zo da shi:

Mu kalli Alkura' ni: Allah ya sabkar da Alkura' ni gare Shi , wanda kuma shine babbar mu'ajiza da Allah ya baShi.

Ina huskokin kasancewar Shi mu'ajiza ne ?

Lalle wannan Alkura' nin mua'jiza ne ta huskoki ma su yawa:

A – mua' jiza ne ta bangaren lafazin Shi, da tsarin Shi, da balagar Shi, tare da awaitar da kalimomi ga ma'anonin da suka date, wannan kwo ya na bayyana ne idan muka kalli mutanen da a ka sabkar da Shi Alkura'ni a cikin su, saboda mutane ne ma su tinkaho da iya magana, kuma Alkura' ni ya kalubalance su da su kawo ko kwotankocin sura daya daga cikin Shii, abin da har yau ya gagari kowa  da kowa.

Me nene tsammanin ka idan ya kasance wanda ya zo da wannan Alkura' ni mutun ne wanda bai san rubutu da karatu ba ! lalle wannan babban dalili ne a kan cewa: Allah ne ya aiko Shi da wannan Alkura' ni zuwa ga mutane da aljannu.

Kuma babba mua' jizar Alkura' ni: kasancewar Shi ya kalubalanci kuraishawa da larabawa da dukan mutane a kan su zo da kamar wannan Alkura' nin, ko kuma su zo da kamar wani daga sharen Shi, abin da tarihi  - a cikin shekara dubu da dari hudu – bai samu wanda ya zo ko da  kamar aya guda daga cikin ayoyin Shi ba, kuma ba za su iya zuwa da ita ba har abada, kuma har yanzu wannan kalubale akwoy shi bai gushe ba, kuma ba zai gushe ba !!!

B - mua' jiza ne ta bangaren ma'anar Shi: lalle Alkura' ni ya na ba da labaren Annabawa da suka gabata ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare su gaba daya) tare da cewa yahudawa su na sauraren Alkura' ni da abin da ya ke labarantarwa game da manzon Allah Musa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ), amma duk da haka ba' a taba samun wani da ga cikin su ya karyata Alkura' ni ba ! muna kuma kara tunatarwa da cewa Muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ummi ne; bai san karatu ko rubutu ba.

Allah ya na cewa: « Kuma ba ka kasance kana karãtun wani littãfi ba a gabãninsa, kuma bã ka rubũtunsa da dãmanka dã haka yã auku, dã mãsu ɓarnã sun yi shakka ». [ Suratul Al-Ankabut 48 ].

An kuma aikwo Shi cikin mutane ne wadanda basu san karatu ko rubutu ba; Allah ya na cewa: « Shĩ ne wanda Ya aika, a cikin mabiya al'ãdu,  wani Manzo daga gare su yanã karanta ãyõyinSa a kansu, kuma yanã tsarkake su, kuma yanã sanar da su littafin da hikimarsa kõ da yake sun kasance daga gabãninsa lalle sunã a cikin ɓata bayyanãnna ». [ Suratul Al-Jumu'ah 2 ].

Kuma Muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ya kasance a Makkah, bai taba barin Makkah ba banda so biyu: da ya tafi sham:

- tafiya ta farko tare da kawun shi abu talib wannan kwa kafin ya balaga, bai kuma rabu da shi ba cikin wannan tafiyar.

- tafiya ta biyu tare da Maisara tafiya ta kasuwanci, yanada shekaru ishirin da 'yan kai, sun kuma kasance tare da mutane da suka san halin shi a cikin wannan tafiyar. Bai taba haduwa ba da wani masani na yahudu ko nasara ko waninsu ba, amma Buhaira malami na nasara da ya gan shi ya gane shi; saboda ya karanta sifofin shi a cikin litattafin su, sai ya sanarda mutanen shi cewa su kula da shi kar yahudawa su cutar da Shi.

Bai taba karatu wajen wani ba; dan haka Allah yake kare shi a cikin Alkura' ni daga zargin wadanda ke tuhumarShi da cewa ya samo shi ne wajen wani mutun.

Allah ya ce: « Kuma lalle ne, haƙĩƙa Munã sanin ( cẽwa ) lalle ne sũ, sunã cẽwa, Abin sani kawai wani mutum ne yake karantar da shi. Harshen wanda suke karkatai da maganar zuwa gare shi, Ba'ajame ne, kuma wannan ( Alƙur'ãni ) harshe ne Balãrabe bayyananne ». [ suratun –nahl 103 ].

A cikin wannan aya Allah ya musu raddi; saboda kaka zai samo wannan alkura' ni daga yahuduwa ko nasara kuma ya kasance da larabci, su kwa ba larabawa ba ne ba.

Kaka mutun mai tarihi kamar haka zai iya zuwa da littafi mai kama haka ?!!

Alkua' ni ya kasance yana mai raddi ga yahudawa wadanda suke Madina game da ayoyin da suka caccanza; kamar da' awar da suke ta cewa Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi) an tsire Shi ne, da fadar wasu daga cikin su cewa Shi dan Allah ne, da fadar wani shashen su cewa Shi mai sihiri ne, haka ma sukar su ga Annabi sulaiman da cewa Shi mai sihiri ne.

Haka ma Alkura' ni yana bada labaren Annabawa da suka gabata ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare su gaba daya) tare da cewa yahudawa suna sauraren Alkura' ni da abin da yake labarantarwa game da manzon Allah Musa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi)  , amma duk da haka ba' a taba samun wani daga cikin su ya karyata Alkura' ni ba !

Kuma a cikin Alkura' ni a kwai annabawa da Attaura da linjila basu zo da kissosin su ba; kamar: Hud, da Salih, da Shu'aib, da wanin wadannan ma.

Haka ma a cikin Alkura' ni muna samun bayani cikakke game da makoma, da wuta da Aljanna, ni'ama da azabar kabari, wadanda babu su a cikin Attaura da linjila !

Game da ababen da Alkura' ni ya ke bada labari a kai na daga ababen da za su abku a gaba, lalle Alkura' ni ya bada labari a kan cewa kawun manzon Allah ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi) Abu lahab zai mutu ba tare da ya yi imani ba, abin da ya kuma abku, tare da cewa shi abu lahab ya ji wannan ayar, amma ko dan ya karyatar da Alkura' ni bai ce ya yi imani ba, ko da a baki !!

Ga kuma wani mai shaida a kan mazoncin Shi: labari da Alkura' ni ya bada game da cewa mutanen rum za su samu nasara a kan farisa, bayan farisawa sun ci su da yaki.

Wannan kwa ya abku kamar yanda Alkura' ni ya fada.

C - Ya na daga cikin mu'ujizar Alkura' ni kasancewar maganganin da ke cikin Shi ba su warware junan su, inda kwa daga wanin Allah ne da an samu sabani mai yawa a cikin Shi.

Allah ma daukaki ya na cewa: « Shin, bã su kula da Alƙur'ãni, kuma dã yã kasance daga wurin wanin Allah haƙĩƙa, dã sun sãmu, a cikinsa, sãɓã wa jũna mai yawa ». [Suratul Al-Nisa 82].

D - Ya na kuma daga cikin mu'ujizar Alkura' ni karfin tasirin Shi ga zukata; domin Shi yana ratsa zuciya ne kamar yanda kibiya ke ratsa abin farauta, haka kuma yana rinjayar kwakwaluwa kamar yanda rana ke rinjayar dufu, wannan kwa masoyi da makiyi sun shaida da shi. Zaka samu makiyi yayin da zai ji Alkura' ni zai saurara miShi kuma zai tasirantu da Shi, kuma zai san cewa wannan ba maganar mutun ce ba.

Al walid dan mugira ya ji karatun Alkura' ni da ga manzon Allah ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi) sai ya ce wa mutanen shi - wadanda sune bani makhzum -: lalle na ji Magana daga Muhammad, amma wannan maganar ba maganar mutun ko aljani ba ce ba, lalle tana da dadi da kayatarwa tare da anfani, gata kuma tana rinjaya kuma ba'a rijayarta.

E - Yana kuma daga cikin mu'ujizar Alkura' ni tasiri da yake yi ga rayuwar musulmi; saboda sun yi aiki da abin da ke cikin Shi, sun kuma yi riko da karantarwar Shi wadda ta ke mai daukaka da tsabta.

Shi Alkura' ni ya daukaka Al – ummar da ta rike Shi ta bangaren karatu da aiki zuwa ga matsayi mai daukaka a huskar ibada da ladubba, sai suka zamanto masu daukaka bayan sun kasance batattu abin rinjaya cikin al – ummomi.

F- Yana kuma daga cikin manya manyan mu'ujizar Alkura' ni tabbatar da ababe na gaibi tamkar imani da Allah da ranar kiyama da manzonni da litattafai … da dalilai na hankali ma su gamsarwa.

Idan kwa ka diba shari' ar da ya zo da ita zaka samu ta kebanta da ababe kamar haka:

1- adalci, domin muslunci ya zo da adalci kuma ya yi hani ga zalunci, ya kuma fara da hana zaluncin dan Adam a karan kan shi, kuma ya haramta dukkan dangogin zalunci ko da a kan dabba ne.

2- shari' ar muslunci ta kuma zo da kare hakin dan adam, da kiyaye tsaron rayukan su da dukiyoyin su, da iyalen su, da hankullan su, da 'yancin su.

3- ta kuma kebanta da cewa ita shari' a ce da ta shafi dukkan bangarori na rayuwa, mai sauki ce ga kowa da kowa, a cikin ta a kwai rahama da jin kai da son juna, ta kuma umarci mutun ya kasance yana da kyawawan dabi' u dan ya kasance abin kauna cikin jama' a.

4- shari' a ta kuma zo da abin da ke sa mutane su ji tausyin junan su; mawadaci ya ji tausayin talakka, ya bashi wani dan karamin kaso daga dukiar shi. Diya su kyautatawa iyayen su, mutun ya kyautatawa makobcin shi, ya kuma sadar da zumuntar shi.

5- mizani na fifiko tsakanin mutane shine tsoran Allah, ba launin fata ko matsayi ba. Mutun yana daukaka da abinda ke tare da shi na imani ne da tsoran Allah, da biyayya ga karantarwar addini.

6- shari' a tana kiran mutun ga kasancewar shi mai anfani a cikin wannan rayuwar, dan haka take umarnin shi da neman ilimi tare da aiki da shi kamar yanda take umarni shi da ya aikata abin da ya ke so mutane su yi mi shi.

7- tana samar da koncin hankali ga dan adam, tana huskantar da hankalin shi da gangar jikin shi zuwa ga abu guda shine neman yardarm mahalittin shi, tsare tsare na muslunci suna samar da daidaituwa da nutsuwa mai ban mamaki ga ran mutun, wannan kwa shi ne sirrin samun koncin hankalin musulmi.

Wanda yake dibin sirrin shigar mutane a muslunci  - musamman ma larabawan da basu san busharar da annabawanda suka gabata suka yi ba game da aiko Shi wannan manzon ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi) – zai samu cewa sun yi imani da Shi ne; saboda ayoyi da alamomi bayyanannu wadanda ke tabbatar da gaskiyar manzoncin Shi, dan haka mabiyan Shi bayan rasuwar Shi, sun fi mabiyan Shi a zamanin Shi yawa so lunkin ba lunki, wannan kwa ba dan kome ba, sai dan tasiri mai kyawo da kayatarwa da muslunci yake sawa a cikin rayuwar mabiyan shi, tare da halayya na gari da yake karantar da su.

Huska ta fudu daga cikin huskoki hudu ita ce: mu'ajizozi da mutun ke samu a gaban shi wadanda kuma suna da yawa, kamar: tsagewar wata, yawaitar da abinci wanda yake kadan, bubbugar ruwa daga yatsotsin shi, kukan kututturan dabino saboda manzon Allah ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi).ya bar huduba da jawabi a kan shi, sallama ta dutsi gare Shi !!! …, da ababe da yawa da malamai suka yi bayani a kai, wadanda suke dalilai ga annabcin Shi ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi).

Ina neman tsarin Allah a kan shaidan abin jifa.

«Yã kũ mutãne! Haƙĩƙa, Manzo yã je muku da gaskiya daga Ubangijinku. Sabõda haka ku yi ĩmãni yã fi zama alhẽri a gare ku. Kuma idan kun kãfirta, to, Allah Yanã da abin da ke cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima »  [Suratul Al-Nisa 170 ].

 

 

Ma rubuci : mut'ab al- harisi