ma'anonin Alkura'ni masu mu'u'jiza


  yabo da godiya sun tabbata ga Allah rayayye mai tsayuwa a kan kome, wanda gyangyadi ko barci ba sa daukarSa, mamallakin dukkan abin da ke cikin sammai da kassai, babu wani mai ceto a gurin Sa face da izinin Sa, yana sanin abin da yake a gaba gare mu da abin da yake baya gare mu, ba ma kewayo ga kome daga ilmin Sa face abin da Ya so, kursiyin Sa ya yalwaci sammai da kasa, kuma tsare su ba ya zama wani nauyi a kan Sa, kuma Shi ne madaukaki mai girma.

Allah ka yi salati ga manzon rahama ka kuma dada masa tsira.

Allah mu na rokon Ka: Ka bamu dukkan abin da ke alkhairi, Ka kuma kiyaye mu da ga dukkan abin da ke sharri gare mu.

manzon Allah ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ya zo da Alkura' ni zuwa ga mutanen Shi, sai kafirai su ka ce: wannan Alkura' nin maganar ka ce ya  kai Muhammad, lalle kai dai ma sihirci ne, ko kuma boka ne kai, ko kuma mahaukaci ne kai, ko kuma ma waki ne kai …

Sai amsa ta zo mu su daga Allah:

 

Allah ma daukaki ya ce: « Kõ sunã cewa: Yã ƙirƙira shi ne. » Ka ce: « Sai ku zo da sũrõri gõma misãlinsa ƙirƙirarru, kuma ku kirãyi wanda kuke iyãwa, baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya ». [ Suratul Hud 13 ].

Allah ya na cewa: « Ka ce: Lalle ne idan mutãne da aljannu sun tãru a kan su zo da misãlin wannan Alƙur'ãni bã zã su zo da misãlinsa ba, kuma kõ dã sãshinsu yã kasance mataimaki ga sãshi ». [ Suratul Al-isra' a 88].

Allah ya kalubalanci kafirai a ko wane lokaci da ko wane guri a kan su zo da ko da kotankocin sura guda daya ta Alkura' ni, abin da ba za su iya ba har abada; domin Alkura' ni mabuwayi ne ta bangarori masu yawan gaske, ga wasu daga cikin wadannan bangarorin ba tare da ambaton dalilen su ba, bayan haka za mu Ambato mahimmai daga cikin su tare da dalilen su:

1 – Alkura' ni mu'u'jiza ne a cikin ababen da yayi bayani a kan su na ilmi, wadanda ilmin zamani ya gano ko zai gano.

2  – Alkura' ni mu'u'jiza ne a cikin ababe na gaibi wadanda za su kasance a gaba ko wadanda su ka kasance a baya, wadanda Ya yi bayani a kan su.

3  – Alkura' ni mu'u'jiza ne ta bangaren cewa Shi daga Allah mahalacci Ya ke, sabanin litattafai da a ka wallafa.

4 – Alkura' ni mu'u'jiza ne ta bangaren cewa ya na da tasiri a kan mai sauraren Shi, har ma wadanda ba su fahintar larabci.

5 – Alkura' ni mu'u'jiza ne ta bangaren watsuwar Shi tsakanin yara da manya, maza da mata, bakake da farare …

6 – Alkura' ni mu'u'jiza ne ta bangaren cewa ya na kira ne zuwa ga dukkan halayya na gari, ya na kuma hani ga dukkan munanen halayya.

7 – Alkura' ni mu'u'jiza ne ta bangaren cewa Shi mai game kome da kome ne ( ma'ana bai manta wani bangare ba ).

8 – Alkura' ni mu'u'jiza ne ta bangaren lafazin Shi da fasahar Shi.

 

Amma abin da ma su hankali su ka hadu a kai shi ne cewa ma'ana tana da fifiko a kan lafazi cikin dukkan Magana.

Dan haka abu mafi muhimmanci shi ne kasancewar Alkura' ni mu'u'jiza ne ta bangaren ababen da suka shafi ma'anonin Sa.

To, ina ma'anonin da Alkura' ni yake kira zuwa gare su ?

 

Amsar ita ce: ma'anonin Alkura' ni ma su mu'u'jiza suna da yawa, a cikin su:

1 – Alkura' ni mu'ajiza ne ta bangaren ya tabbatar da cewa a kwai Allah, wanda Shi ne mahalacci, mai arzutawa, wannan ko tare da dalillai ma su gansarwa, lokacin da kafirai su ka kasa tabbatar da rishin Shi wannan Ubangijin wanda ke mahallaci.

Dan haka Allah a cikin Alkura' ni so da yawa yana tambayar kafirai: wa ya halitti abu kaza ?  wa ya halitti abu kaza ?   …

Ga wasu dalilai na hankali da Alkura' ni ya kawo game da wannan ma'anar mai girma.

 

Allah Y ace:

 

« Kuma lalle ne, idan ka tambaye su: Wãne ne ya halitta sammai da ƙasa? Lalle zã su ce, Mabuwãyi Mai ilmi ne Ya halitta su. 
Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa kuma Ya sanya muku hanyõyi a cikinta, tsammãninku za ku nẽmi shiryuwa.'

Kuma Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, a kan wani gwargwado, sai Muka rãyar da gari matacce game da shi. Kamar haka nan ake fitar da ku ( daga kabari ) . 
Kuma Wanda Ya halitta ma'aura dukansu, kuma Ya sanya muku, daga jirgi da dabbõbin ni'ima, abin da kuke hawa. 
Domin ku daidaitu a kan bãyansa, sa'an nan ku tuna ni'imar Ubangijinku a lõkacin da kuka daidaita a kansa kuma ku ce: Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hõre mana wannan alhãli kuwa ba mu kasance mãsu iya rinjãya gare Shi ba. 
Kuma lalle mũ haƙĩƙa mãsu jũyãwa muke, zuwa ga Ubangijinmu ». [ Sũratuz Zukhruf 9 -14 ].

Allah ma daukaki ya kuma ce: « Yaya kuke kãfirta da Allah, alhãli kuwa kun kasance matattu sa'an nan Ya rãyar da ku, sa'nnan kuma Ya matar da ku, sa'an nan kuma Ya rãya ku, sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku? 
Shi ne Wanda Ya halitta muku abin da ke a cikin ƙasa gaba ɗaya, sa'an nan kuma Ya daidaita zuwa sama, sa'an nan Y a aikata su sammai bakwai. Kuma Shi ga dukan kõmai Masani ne ».  [ Suratul Al-Baqarah 28 – 29 ].

Allah ma daukaki ya kuma ce: « 3. Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya. Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka. 
4. Ya halicci mutum daga maniyyi, sai gã shi yanã mai husũma bayyananniya. 
5. Da dabbõbin ni'ima, Ya halicce su dõminku. A cikinsu akwai abin yin ɗumi da waɗansu amfãnõni, kuma daga gare su kuke ci. 
6. Kuma kunã da kyau a cikinsu a lõkacin da suke kõmõwa daga kĩwo da maraice da lõkacin da suke sakuwã

7. Kuma sunã ɗaukar kãyanku mãsu nauyi zuwa ga wani gari, ba ku kasance mãsu isa gare shi ba, fãce da tsananin wahalar rãyuka, Lalle ne Ubangijinka ne, haƙĩƙa, Mai tausayi, Maijin ƙai. 
8. Kuma da dawãki da alfadarai da jãkuna, dõmin ku hau su, kuma da ƙawa. Kuma Yana halitta abin da ba ku sani ba. 
9. Kuma ga Allah madaidaiciyar hanya take kuma daga gare ta akwai mai karkacẽwa. Kuma da Yã so, dã Ya shiryar da ku gabã ɗaya. 
10. Shĩ ne Wanda Ya saukar da ruwa daga sama dõminku, daga gare shi akwai abin sha, kuma daga gare shi itãce yake, a cikinsa kuke yin kĩwo. 
11. Yanã tsirar da shũka game da shi, dõminku zaitũni da dabĩnai da inabai, kuma daga dukan 'yã'yan itãce. Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke yin tunãni. 
12. Kuma Ya hõrẽ muku dare da wuni da rãnã da watã kuma taurãri hõrarru ne da umurninSa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke hankalta. 
13. Kuma abin da Ya halitta muku a cikin ƙasa, yana mai sãɓãnin launukansa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke tunãwa. 
14. Kuma Shĩ ne Ya hõrẽ tẽku dõmin ku ci wani nama sãbõ daga gare shi, kuma kunã fitarwa, daga gare shi, ƙawã wadda kuke yin ado da ita. Kuma kuna ganin jirãge sunã yankan ruwa a cikinsa kuma dõmin ku yi nẽman ( fatauci ) daga falalarSa. Kuma mai yiwuwa ne kuna gõdẽwa.

15. Kuma Ya jẽfa, a cikin ƙasa, tabbatattun duwatsu dõmin kada ta karkata da ku, da kõguna da hanyõyi, ɗammãninku kunã shiryuwa. 
16. Kuma da waɗansu alãmõmi, kuma da taurãri sunã mãsu nẽman shiryuwa ( ga tafiyarsu ta fatauci ) . 
17. Shin, wanda Yake yin halitta yanã yin kama da wanda ba ya yin halitta? Shin fa, bã ku tunãwa? 
18. Kuma idan kun ƙidãya ni'imar Allah, bã ku iya lissafa ta. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai …

65. Kuma Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta. Lalle ne a cikin wannan haƙĩƙa akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke saurãre. 
66. Kuma lalle ne, kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'ima;Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikin cikunansu, daga tsakãnin tukar tumbi da jini nõno tsantsan mai sauƙin haɗiya ga mãsu shã. 
67. Kuma daga 'ya'yan itãcen dabĩno da inabi. Kunã sãmudaga gare shi, abin mãye da abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta. 
68. Kuma Ubangjinka Yã yi wahayi zuwa ga ƙudan zuma cẽwa: « Ki riƙi gidãje daga duwãtsu, kuma daga itãce, kuma daga abin da suke ginãwa. » 
69. « Sa'an nan ki ci daga dukan 'ya'yan itãce, sabõda haka ki shiga hanyõyin Ubangijinka, sunã hõrarru. » Wani abin shã yanã fita daga cikunanta, mai sãɓãwar launukansa a cikinsa akwai wata warkewa ga mutãne. Lalle ne, a cikin wannan, haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni. 
70. Kuma Allah ne Ya halicce ku, sa'an nan Yanã karɓar rãyukanku, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwã zuwa ga mafi ƙasƙncin rãyuwa, dõmin kada ya san kõme a bãyan dã ya zama mai ilmi. Lalle Allah ne Masani Mai ĩkon yi. 
71. Kuma Allah Ya fifita sãshenku a kan sãshe a arziki. Sa'an nan waɗanda aka fĩfĩta ba su zama mãsu mayar da arzikinsu a kan abin da hannãyensu na dãma suka mallaka ba, har su zama daidai a cikinsa. Shin fa, da ni'imar Allah suke musu? 
72. Kuma Allah Yã sanya muku mãtan aure daga kãwunanku, kuma Ya sanya muku daga mãtan aurenku ɗiyã da jĩkõki, kuma Ya arzũta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Shin fa, da ƙarya suke yin ĩmãni, kuma da ni'imar Allah sũ, suke kãfirta? …

78. Kuma Allah ne Ya fitar da ku daga cikunan iyãyenku, ba da kunã sanin kõme ba, kuma Ya sanya muku ji da gannai da zukãta, tsammãninku zã ku gõde. 
79. Shin ba su ga tsuntsãye ba sunã hõrarru cikin sararin sama bãbu abin da yake riƙe su fãce Allah? Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.

80. Kuma Allah ne Ya sanya muku daga gidajenku wurin natsuwa, kuma Ya sanya muku daga fatun dabbõbin ni'ima wasu gidãje kunã ɗaukar su da sauƙi a rãnar tafiyarku da rãnar zamanku, kuma daga sũfinsu  da gãshinsu da gẽzarsu ( Allah ) Ya sanya muku kãyan ɗãki da na jin dãɗi zuwa ga wani lõƙaci. 
81. Kuma Allah ne Ya sanyã muku inuwa daga abin da Ya halitta, kuma Ya sanyã muku ɗãkuna daga duwãtsu, kuma Ya sanyã muku waɗansu riguna sunã tsare muku zãfi, da waɗansu rĩguna sunã tsare muku makãminku. Kamar wancan ne ( Allah ) Yake cika ni'imarSa a kanku, tsammãnin ku, kuna sallamawa. 
82. To, idan sun jũya, to, abin da ya wajaba a kanka, shi ne iyarwã kawai, bayyananniyã.

83. Suna sanin ni'imar Allah, sa'an nan kuma sunã musunta, kuma mafi yawansu kãfirai ne ».  [Suratul Al-Nahl].

2 – Alkura' ni mu'u'jiza ne; domin Ya zo da hujjoji na hankali a kan cewa babu wani abin bautawa da gaskiya face Allah. Sa' an nan kafirai sun gaza, kuma ba za su taba zuwa da hujja ko da guda daya ba wadda ke nuna cewa wanin Allah ya yi halitta irin ta Allah, ko kuma yake da tarayya da Allah a cikin halittar Sa, ko ya taimakawa Allah cikin halittar sammai da kassai, ko kuma yake wakiltar Allah a cikin gudanar da al – amurra.

Ga wasu dalilai na hankali da Alkura' ni ya zo da su a kan haka:

Allah madaukaki ya na cewa:  « 10. ( Allah ) Ya halitta sammai, bã da ginshiƙi wanda kuke gani ba, kuma Yã jẽfa duwatsu mãsu kafuwa a cikin ƙasã, dõmin kada ta karkata da ku kuma Ya wãtsa daga kowanc irin dabba a cikinta, kuma Mun saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka tsirar a cikinta, daga kõwane nau'i biyu ( nami; i da mace ) mai ban sha'awa. 
11. Wannan shĩ ne halittar Allah. To ku nũna mini, Mẽne ne waɗanan da ba Shi ba suka halitta? Ã'a, azzalumai sunã a cikin ɓata bayyananna ».[ Suratul luqman].

Allah ya na kuma cewa: « Allah bai riƙi wani abin haihuwa ba, kuma bãbu wani abin bautãwa tãre da Shi. Idan haka ne ( akwai abin bautawa tare da Shi ) , lalle ne dã kõwane abin bautawar ya tafi da abin da ya halitta, kuma lalle ne, dã waɗansu sun rinjãya a kan waɗansu, tsarki ya tabbata ga Allah, daga abin da suke siffantãwa ».[ Suratul Al-Mu'minun 91].

Allah ya na kuma cewa: « Ka ce: Dã akwai waɗansu abũbuwan bautãwa tãre da shi, kamar yadda suka faɗa, a lõkacin, dã ( abũbuwan bautãwar ) sun nẽmi wata hanya zuwa ga Ma'abũcin Al'arshi ». [ Suratul Isra 42 ].

Allah ya na kuma cewa: « Ka ce: Ku kirãyi waɗanda kuka riya ( cẽwa abũbuwan bautãwa ne ) baicin Allah, bã su Mallakar ma'aunin zarra a cikin sammai, kuma bã su Mallakarsa a cikin ƙasa kuma bã su da wani rabon tãrẽwa a cikinsu ( sammai da ƙasa ) ,kuma bã Shi da wani mataimaki daga gare su ». [Suratu- Saba 22].

Allah ya na kuma cewa: « 22 Dã waɗansu abũbuwan bautawa sun kasance a cikinsu  ( sama da ƙasa ) fãce Allah, haƙĩƙa dã su biyun sun ɓãci. Sabõda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al'arshi daga abin da suke siffantãwa.

23. Bã a tambayar Sa ga abin da Yake aikatãwa, alhãli kuwa sũanã tambayar su. 
24. Kõ sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa baicinSa? Ka ce: « Ku kãwo hujjarku, wannan shi ne ambaton wanda yake tãre da ni, kuma shi ne ambaton wanda yake a gabãnĩna. Ã'a, mafi yawansubã su sanin gaskiya, sabõda haka sũ mãsu bijirẽwa ne ».   [ Suratul Al-Anbiya ].

Allah ya na kuma cewa: « Allah Yã buga misãli; wani mutum ( bãwa ) a cikinsa akwai mãsu tarayya, mãsu mũgun hãlin jãyayya, da wani mutum ( bãwa ) dukansa ga wani mutum. Shin, zã su daidaita ga misãli? Gõdiya ta tabbata ga Allah ( a kan bayãni ) . Ã'a, mafi yawan mutãne ba su sani ba ». [ Suratul Al-Zumar 29].

3- Alkura' ni mu'u'jiza ne ta bangaren ya sanar da cewa akwai wata rana da Allah zai sake tada halittu saboda Ya sakauta musu a kan ayukkan su; wanda ya aikata aiki na gari ya samu Aljanna, wanda kuma ya aikata mummunan aiki ya samu azaba ta wuta.

Dalilai da Alkura' ni Ya kawo a kan hakan suna da yawa; za mu takaita a kan guda daya a cikin surar yasin:

Aallah madaukaki Yana cewa: « 78.  Kuma ya buga Mana wani misãli, kuma ya manta da halittarsa, ya ce: Wãne ne ke rãyar da ƙasũsuwa alhãli kuwa sunã rududdugaggu?

Ka ce: Wanda ya ƙãga halittarsu a farkon lõkaci Shĩ ke rãyar da su ». [ Suratul Ya-Sin 78 – 79 ].

Wannan hujja ce ta hankali: wanda ya yi halitta ta farko, ta biyu ba zata gagare Shi ba.

Karshen ayoyin: « kuma Shi, game da kõwace halitta, Mai ilmi ne.

Wanda ya sanya muku wutã daga itãce kõre, sai gã ku kunã kunnãwa daga gare shi. »

Wannan wata hujjar ce ta hankali: wanda ya hada mu'u'jizozi masu karo da juna ( fitar da wuta daga koren itace da ke cike da ruwa ! ); wanda ya yi hakkan, halitta ta biyu ba zata taba buwayar Sa ba.

Ya kuma ci gaba da cewa: « Shin, kuma Wanda Ya halitta sammai da ƙasã bai zama Mai ĩkon yi ba ga Ya halitta kwatankwacinsu? ».

Wannan kuma wata hujja ce ta wata huskar: wanda ya halicci sammai da kasa alhali kwa sun fi girma mai iko ne a kan maida halittar wanda yake kankane kamar dan Adam.

Ya kuma ci gaba da cewa: « Na'am, zai iya! Kuma Shĩ Mai yawan halittãwa ne,Mai ilmi. 
82. UmurninSa idan Yã yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai, « Ka kasance, » sai yana kasancewa ( kamar yadda Yake nufi ) .

83. Sabõda haka, tsarki yã tabbata ga Wanda mallakar kõwane abu take ga HannãyenSa, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku ».

 

Ma rubuci : Bandar Ahmad