Daga cikin wasiyoyin Alkura'ni  ( mai girma ): wasiyoyi goma


قال الله تعالى في سورة الأنعام :

 

{ قُلْ تَعَالَوْا أَتْلُ مَا حَرَّمَ رَبُّكُمْ عَلَيْكُمْ أَلَّا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا وَلَا تَقْتُلُوا أَوْلَادَكُمْ مِنْ إِمْلَاقٍ نَحْنُ نَرْزُقُكُمْ وَإِيَّاهُمْ وَلَا تَقْرَبُوا الْفَوَاحِشَ مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَمَا بَطَنَ وَلَا تَقْتُلُوا النَّفْسَ الَّتِي حَرَّمَ اللَّهُ إِلَّا بِالْحَقِّ ذَلِكُمْ وَصَّاكُمْ بِهِ لَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ (151) وَلَا تَقْرَبُوا مَالَ الْيَتِيمِ إِلَّا بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ حَتَّى يَبْلُغَ أَشُدَّهُ وَأَوْفُوا الْكَيْلَ وَالْمِيزَانَ بِالْقِسْطِ لَا نُكَلِّفُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا وَإِذَا قُلْتُمْ فَاعْدِلُوا وَلَوْ كَانَ ذَا قُرْبَى وَبِعَهْدِ اللَّهِ أَوْفُوا ذَلِكُمْ وَصَّاكُمْ بِهِ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ (152) وَأَنَّ هَذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيمًا فَاتَّبِعُوهُ وَلَا تَتَّبِعُوا السُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمْ عَنْ سَبِيلِهِ ذَلِكُمْ وَصَّاكُمْ بِهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ (153)}.

 

Allah madaukaki Yana cewa a cikin suratul Am'am:

 

(( 151. Ka ce: « Ku zo, in karanta abin da Ubangijinku Ya haramta. » wãjibi ne a kanku kada ku yi shirkin kõme da Shi, kuma ga mahaifa biyu ( ku kyautata ) kyautatãwa, kuma kada ku kashe ɗiyanku sabõda talauci, Mũ ne Muke azurta ku, kũ da su, kuma kada ku kusanci abũbuwa alfãsha, abin da ya bayyana daga gare ta da abin da ya ɓõyu, kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta, fãce da hakki. Wannan ne ( Allah ) Ya yi muku wasiyya da Shi: Tsammãninku, kunã hankalta. 
Wahayin shaiɗan zuwa ga mãsu shirki da hana dabbõbi da ƙãga wasu hukunce- hukunce. Kalmar gaskiya ce ake yin nufiƙarya da ita, da bãyanin warware rikicin. Jũyar damaganar gaskiya dõmin a yi ƙarya da ita yanã sabbaba saukar azãba. Kuma dukan maganar da bã ta da asali ga Littãfi kõ sunna, to, bã gaskiya ba ce, bin ta nau'in shirki ne.

 

152. Kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga ƙarfinsa. Kuma ku cika mũdu da sikli da ãdalci, bã Mu kallafã wa rai fãce iyãwarsa. Kuma idan kun faɗi magana, to, ku yi ãdalci, kuma ko dã yã kasance ma'abũcin zumunta ne. Kuma da alkawarin Allah ku cika. wannan ne Ya yi muku wasiyya da shi: Tsammãninku, kunã tunãwa. 
153. Kuma lalle wannan ne tafarkĩNa, yana madaidaici: Sai ku bĩ shi, kuma kada ku bi wasu hanyõyi, su rarrabu da ku daga barin hanyãTa. Wannan ne Allah Ya yi muku wasiyya da shi tsammãninku, kunã yin ta
ƙawa )).

 

 

،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،،

 

Allah (madaukaki) Yana cewa manzon Sa ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) da duk wanda ke kira zuwa ga addinin muslunci: ( ka ce: ) wa dukkan mutane (« Ku zo, in karanta abin da Ubangijinku Ya haramta. ») haramci wanda yana hada kowa da kowa, ya kuma kunshi dukkan ababen da ke haram, na daga cimaka da abin sha da maganganu da ayukka.

wasiyoyi goma sune : *

wasiya ta farko:  (wãjibi ne a kanku kada ku yi shirkin kõme da Shi);

abin nifi kada ku hada Allah da wani a cikin bauta; kadan ko da yawa. Hakikanin shi shine a bautawa abin halitta tamkar yanda ake bautawa Allah, ko a girmama shi kamar yanda ake girmama Allah, ko a sanya maSa wani abu da Allah Ya kebanta da shi na daga rububiya ko uluhiyya. Idan bawa ya guji shirka gaba daya sai ya kasance mai kadaitar da Allah, mai ikhlasi ga Allah a cikin dukan halayen shi; wannan kuma shi ne hakkin Allah akan bayin Sa: su bauta miSa, ba tare da hada Shi da wani cikin wata bauta ba.

Duk wanda ya yi da'awar wani abin bauta koma bayan Allah, to lalle ya nemi tauye Allah a cikin milkin Sa, da karfin Sa, da daukakar Sa, amma wanda bai yi shirka ba, to lalle ya yi imani da cewa Allah shine makadaici mai rinjaye, mai milki, ma buwayi. Allah mai tsarki Yana cewa: « 27. Ka ce: Ku nũna mini waɗanda kuka riskar da Shi, su zama abõkan tãrayya. Ã'a, Shĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima ». (suratu sabai )

 

wasiya ta biyu: (kuma ga mahaifa biyu ( ku kyautata ) kyautatãwa);

sa' annan ya fara da mafi girman hakki bayan hakkin Shi –tsarki da daukaka sun tabbata a gare Shi- wanda shine hakkin ma aifa, sai Ya yi umarni da a kyautata masu da Magana mai kyau kuma da ayukka kyawawa; dukkan Magana ko aiki wanda ke da anfani gare su ko yake faranta musu da rai ya na daga cikin kyautatawa, idan kwa aka samu kyautatawa to lalle sabawa iyaye zai gushe. Farin ciki ya tabbata ga wanda ya yi biyayya ga iyayen shi, wanda kwa ya sabawa iyaye ya kuka da kan sa, ya komo kan hanya.

 

wasiya ta uku: (kuma kada ku kashe ɗiyanku sabõda talauci, Mũ ne Muke azurta ku, kũ da su);

kada ku kashe diyan ku, maza ko mata, saboda tsoron talauci da kuncin rayuwa, tamkar yanda ya kasance a lokacin jahiliya. Idan kwa ya kasance an yi hani ga kisan su a cikin halin talauci, to kisan su ba tare da talauci ba shine ma fi muni, haka ne kuma kashe diya wadanda ke ba nasu ba.

Allah Ya ce: ( mu ne mu ke arzita ku, ku da su); abin nifi: mune muka dau dawainiyar arzuta kowa da kowa, ba kune ke arzuta diyan naku ba, hasali ma ba kune ke arzuta kanun ku ba, dan haka basu zama kunci a gare ku ba.

 

wasiya ta hudu:  ( kuma kada ku kusanci abũbuwa alfãsha, abin da ya bayyana daga gare ta da abin da ya ɓõyu ); 

alfasha sune manya manyan zunubbai; wadanda suke a bayyane da wadanda suke a boye; abin nifi kad ku kusance su, kuma hani ga kusantar su shine yafi kai matuka a kan hani ga barin su, domin ya kunshi hani ga ababen da ke gabatar su, da hanyoyin da ke kaiwa gare su.

 

wasiya ta biyar: ( kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta, fãce da hakki ); 

abin nifi ran musulmi, namiji ko mace, babba ko yaro, mai biyayya ko mai sabo, ko kafiri wanda jinin shi ya kariya ta hanyar yin alkawali da musulmi.

(Face da hakki); tamkar wanda ya yi zina alhali kwa ya taba yin aure, ko wanda ya yi kisan kai, ko wanda ya yi ridda ya fita daga muslunci.

 

Wadannan ababe da suka gabata sune ababen da Allah Ya yi wasici a kan su; domin ku hankalce su: ku kiyaye su kuma ku yi aiki da su.

Kuma ayar tana nuni akan cewa dan adam yana kiyaye su ne gwargwadon karfin hankalin sa.

 

wasiya ta shida: (Kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga ƙarfinsa );

abin nifi: kada ku kusanci dukiyar maraya, ta hanyar ci, ko abin da ya yi kama da haka, ba tare da wani sababi ba, sai dai idan ya kasance ta hanya kyakyawa; kamar halin bunkasa ta ta hanyar kasuwanci..

ayar tana nuni akan cewa bai halitta a kusanci dukiyar maraya ba sai dai ta hanyar da za ta anfane shi kuma ba za ta cutar da shi ba.

Wannan kwa har sai ya balaga ya shiga hankalin sa, idan ya balaga kuma hankalin shi ya cika sai a bashi dukiyar sa, ya juya ta yanda yake so.

 

wasiya ta bakwai: (Kuma ku cika mũdu da sikli da ãdalci ); idan ku ka yi kwokarin ku akan haka haka (bã Mu kallafã wa rai fãce iyãwarsa ); abin da ba zai kuntata mata ba. Duk wanda ya yi kwokarin shi wajen cika ma'auni, sa'annan aka samu tawayar ma'aunin ba tare da nifi ba, to lalle Allah mai afuwa ne, mai yawan gafara.

Da kuma wannan ayar da makamantar ta ne malamai suka kafa hujja akan cewa Allah ba Ya dora wa rai abin da ba za ta iya ba; wanda ya ji tsoron Allah daidai gwargwodo a cikin abin da aka umarce shi, Allah ba Ya kama shi akan abin da ba shi da iko a kai.

 

wasiya ta takwas: (Kuma idan kun faɗi magana, to, ku yi ãdalci, kuma ko dã yã kasance ma'abũcin zumunta ne );

idan za ku yi hukunci tsakanin ma su rigima, ko kuma za ku yi magana to ku yi adalci a cikin hukuncin ko maganar, ku kiyaye gaskiya ba tare da banbanci ba tsakanin wanda ku ke so da wanda ba kwa so ba, kuma ku bayyana dukkan abin da ku ka sani ba tare da bangaranci ba; saboda karkata zuwa ga wanda ku ke so zalunci ne.

dan haka malamai su ka ce: ya zama wajibi akan alkali ya daidaita tsakanin abokanen hamayya har ma a wajen magana da kallo.

 

 

wasiya ta tara: (Kuma da alkawarin Allah ku cika );

wannan ya kunshi alkawarin da bayi suka dauka na cika kakkokin Allah, kuma ya kunshi alkawura dake tsakanin bayi; dukan su wajibi ne a cika su, kuma bai halitta a saba daya daga cikin su ba.

 

(wannan ne) ma'ana wadannan hukunce hukunce sune ( Ya yi muku wasiyya da su; Tsammãnin cewa za ku kunã, tunãwa);tuna abin da Ya bayyana muku na daga hukunce hukunce, kuma ku aikata wasiyar Allah yanda ya kamata, kuna abin da ta kunsa.

Yayin da Ya bayyana manya manyan umarni, da ababen shar'antawa ma su muhimmanci, sai Ya yi nuni ga abin da ke game dukkan abin da ya gabata a cikin;

 

wasiya ta goma sai Ya ce: (Kuma lalle wannan ne tafarkĩNa, yana madaidaici: Sai ku bĩ shi) ma'ana sai ku bi wadannan kukunce hukunce da abin da ya yi kama da su, wadanda ke cikin Alkura'ni  da sunnah, wadanda sune ke kaiwa ga gacci: gidan girmamawa wanda ke shine gidan aljanna.

 

(Sai ku bĩ shi) dan ku samu rabo da dadin kai (kuma kada ku bi wasu hanyõyi) wadanda suka saba wa wannan hanyar (su rarrabu da ku daga barin hanyãTa) su batar da ku, sai ku kasance a cikin dimuwa da fagamniya, daga karshe ku samu kanku a cikin azaba mai radadi a cikin jahannama.

 

(Wannan ne Allah Ya yi muku wasiyya da shi tsammãninku, kunã yin taƙawa); idan ku ka yi aiki da wadannan wasiyoyi za ku kasance cikin ma su takawa, bayin Allah ma su babban rabo. Kuma wannan hanyar guda daya ce, dan haka Ya ce: (wannan ita ce hanya ta); hanya guda ba ta da ta biyu.

 

(ku diba tafsirin wannan aya a cikin tafsirin abdurrahman ibn Nasir As Sa'adi ) 

 

A karshe ga wadannan wasiyoyi a takaice; dan mu fara aiki da su mu duka, a nan gidan duniya, sai mu samu sakamakon aikin mu a lahira da yardar Allah (ma daukaki ) a cikin gidan Aljanna!

 

wasiyoyi goma sune :

wasiya ta farko:  (kada ku yi shirkin kõme da Shi); 

kada ku hada Shi da wani a cikin bauta, ku sanya dukkan ibadar ku gare Shi, Shi kadai; tamkar so da kauna, da adu'a, da abin da ya yi kama da haka.

 

wasiya ta biyu: ( kuma ga mahaifa biyu ( ku kyautata ) kyautatãwa)ku kyautata ta hanyar biyayya, da adu'a, da abin da ya yi kama da haka. 

 

wasiya ta uku: (kuma kada ku kashe ɗiyanku sabõda talauci, Mũ ne Muke azurta ku, kũ da su )kada ku kashe diyan ku saboda talauci da ku ke fama da shi, Allah Shi ne mai arzutar da ku da su gaba daya. 

wasiya ta hudu: (kuma kada ku kusanci abũbuwa alfãsha, abin da ya bayyana daga gare ta da abin da ya ɓõyu ); kada ku kusanci abin da ya bayyana ko yake a boye daga manya manyan zunubbai. 

wasiya ta biyar: (kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta, fãce da hakki ); kashe ta da hakki yana kasancewa ne a halin kisasi, ko zina bayan aure, ko ridda daga muslunci. 

wasiya ta shida: (Kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga ƙarfinsa)abin nifi ta hanyar bunkasa wannan dukiyar har sai marayan nan ya balaga kuma ya shiga hankalin sa, bayan haka sai a bashi dukiyar sa. 

wasiya ta bakwai: (Kuma ku cika mũdu da sikli da ãdalci ); ku cika ma'auni da mudu da adalci. 

wasiya ta takwas: (Kuma idan kun faɗi magana, to, ku yi ãdalci, kuma ko dã yã kasance ma'abũcin zumunta ne ); abin nifi ba tare da karkata ba shin cikin bada labari ne, ko shaida ne, ko ceto ne, ko da kwa wannan wanda maganan nan ta shafa ya kasance ma abocin zumunci ne, ku fadi gaskiya. 

wasiya ta tara: (Kuma da alkawarin Allah ku cika )alkawarin da ku ka dauka na cewa za ku yi riko da shari'ar Sa. 

wasiya ta goma: (Kuma lalle wannan ne tafarkĩNa, yana madaidaici: Sai ku bĩ shi, kuma kada ku bi wasu hanyõyi, su rarrabu da ku daga barin hanyãTa); daga cikin ababen da Allah Ya muku wasici akwai cewa wannan musluncin shine hanyar Allah wadda ke a mike, ba ta da karkata, dan haka ku bita; dan ku kiyaye wutar Sa, wannan kwa ta hanyar bin umarnin Sa, da barin abin da Ya ce a bari. 

Wanda ya hada wannan bayani shine: Mut'ab Al Harisi