Me ya sa mace musulma take sanya hijabi ?


Me ya sa mace musulma take sanya hijabi ?"

 

Mutane da yawa suna tambaya: me ya sa mace musulma take sanya hijaba ? Kaka a kayi ta yarda da saka shi ?

 

Amsa ita ce: duk wanda ya yarda da muslunci, ya kuma yarda da cewa shi addinin gaskiya ne da Allah madaukaki ya sabkar ga manzon shi Muhammad ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) zai yarda da  wannan hukuncin, yarda da hankalin shi da ingancin dukkan abin da muslinci ya zo da shi. Wannan kwa domin shi hankali shine ya nuna masa cewa muslunci shine addinni na gaskiya, to kenan sai ya yarda da dukkan abin da muslunci ya zo da shi, saboda ya san cewa wanda ya sabkar da wannan addini –wanda ke shine Allah mai girma- ya fi ababen halitta sanin  abin da zai anfane su; kuma saboda haka Ya sanya musu tsari da ya dace da su.

Amma game da amsar tambayar me ya sa mace musulma take sanya hijabi ? amsar ita ce: idan muka diba anfanin shi hijabin ga mace, ko kuma  ma  ga namiji, za muga cewa anfani ne mai yawa.

 

Yana da anfani ga mace; domin yana maida ita abu mai tsada, abin lullubewa saboda muhimmancin shi, abin da mutane  ba za su iya wasa das hi ba.

 

Wannan abin mai tsada ana lullube shi ne dan a bashi darajar da ta kamace shi, kuma dan a kiyaye shi daga wasan masu wasa. Haka ne shi ma muslunci ya lullube mace domin ya kareta daga sharrin dukkan masu sharri, kuma daga yaudarar dukkan mayaudara.

 

Abu na biyu kuma shine: mace yayin da tayi aure ba ta son mijin ta ya dinga kallon mata; domin kar ya ga wacce ta fi ta kyawo; kenan samar da wannan hijabin zai sa namijin nan ba zai ga wata mace ba, barantana ma har ya ga wacce ta fi matar shi kyawo, har hankalin shi ya koma gare ta.

 

Sa' an nan kuma yanada anfani ga namiji; domin yana kiyaye mishi lokacin shi da kokarin shi, sai ya sanya shi cikin wani abu mai anfani maimakon ya tafiyar da shi a wajen kallon matan da ba su halitta ba gare shi.

 

Kuma yana da anfani ga namiji; domin zai kare shi daga ganin wata mace wadda zata dau hankalin shi, kuma ta fitnance shi, alhali, kwa yana da mata, ita kuma tana da miji, wanda kuma hakan zai iya kaiwa ga roshewar gidaje, da kuma halakar mata da maza da yawa; dan haka muslunci ya rife wannan kofar gaba dayan ta; sai ya umarci mace da ta rufe huskar ta, kamar yanda ya umarci namiji da ya kiyaye ganin shi.