Minene Muslunci?  Yaya ake shiga Muslunci?


Muslunci
 
Minene Muslunci?  Yaya ake shiga Muslunci?
 
   Dukkan addini na gaskiya ko na karya, dukkan jam'iya mai anfani ko mai cutarwa, dukkan kungiya mai  alkhairi ko mai sharri… 
Dukkan wadan nan suna da akidodin su da kuma ginshikai da manufofin manufofin su, manufofi da ke  zama kamar  kundi ga mabiyan su.
Idan mutun yana son shiga cikin ko wane daya daga ababen da suka gabata, abu na farko da yake dibawa shine wadanan akidodi da gimshikai, idan ya yarda da su, kuma ya kudurcesu ba tare da shakku ba, bayan ya fahimci abinda suka kumsa, sai ya mika wuya, ya kuma zama daya daga ma biya wanan kungiya ko addinni. Bayan haka sai ya kasance wajibi akan shi ayukkan da ke wajibi akansu, ya kuma nisanci ababen da shi wanan kundi ya kumsa tare da ikhlasi a cikin dukkan ayukanshi a kowane lokaci, ya na mai  kira zuwa gare shi.
Kasancewar mutun a cikin wanan kungiyar yana nufin ya san dokokin wanan kungiyar, ya kuma kudurci manufofinta, bayan haka ya yarda da hukunce hukuncen ta,  tare da bayyana wadannan dokoki da hukunce hukumce a aikace. haka ne Muslunci ma.
Wanda yake son shiga cikin muslunci ya zama wajibi a kansa yayi imani da kudurce kudurce na muslunci dan ya kasance ya na akida ta muslunci.
Wanan  akida ta kunshi imani da kasancewar wannan duniyar da muke gani ba ita ce kway ba, akoy abubuwa wa 'ynda ba ma ganinsu, akoy kuma wata rayuwa bayan wannan rayuwar ta duniya.
Dan adam bai samar da kanshi ba, bayan haka wani abun halitta bai samarda shi ba, ba wanda ya samarda shi banda ubangijin da ya samarda halittu gaba dai bayan babu su, wandake bada rayuwa ko mutuwa, shine Allah wanda ya halicci kowa da kome, idan kuma yaso sai ya kasha su gaba daya,  wanda babu mai  kama da shi, babu wani abu da yake buya gareshi, shine na farko babu wani abu gabaninsa, shine kuma na karshe babu wani abu bayansa, shine mai  ikon da ba shi da iyaka, shine mai  adalcin da bay a kama da adalcin ababen halitta.
Shine ya saka ka idodi na dabi ia da rayuwa ke tafiya a kai , ya kuma sanya kome a matsayin sa da ya cancanta tun fil azal, ya kaddara motsi ko aiki da rashin su, yakuma baiwa da adam hankali da yake gane abubuwa da yawa da shi, wanda kuma da shine Allah ya bashi damar zabin abin da yake so a cikin rayuwa.
Bayan wannan rayuwar takaitatta ya sanya wata rayuwa wadda take mai  dorewa ita ce lahira domin ya sakauta wa masu biyayya gare Shi a kan ayukkan su nagari da aljanna, wadanda suka ki biyayya kwa da jahannama.
Allannan shi daya yake ba shi da abokin tarayya, bai sanya tsani tsakanin shi da bayin Sa ba, babu mai ceto agurin Sa ba tare da izinin Sa ba, Shi kadai ake wa bawta, ko wan irin bawta ne.
Ya nada ababen halitta wadanda muke ganin su kamar yanda yake da halittu, masu motsi da wadanda ba sa motsi, da ba ma ganin su.
Halittun Sa sun kasu kishi uku:
Masu alkhairi kadai ( su ne mala' iku ).
Masu sharri kadai ( su ne shaidannu ).
Wadanda suka hada alkhairi da sharri  ( aljani da mutun ).
Allah ya na zaben wasu mutane wadanda mala' ikun Sa ke sabkar da shari' a gare su domin su isar da ita ga al – ummomin su; wadannan mutane su ne manzonni. 
Shari' a ta karshe daga cikin Shari' o' in nan ( shari' ar musulunci ) ta shafe dukkan Shari' o' in da suka gabace ta, dan haka littafi na karshe da Allah ya sabkar shine Alkur' ani , wanda ya  kore dukkan litattafen da suka zo gabanin shi, domin litattafen nan an cancanza su, wadan su kuma sun bace, wasu kuma an manta su; Alkur' ani kadai ne ya kubuta daga ababen da su ka gabata.
Kuma hake ne muhamad ( tsira da rahama ta musamman su tabbata a gare shi, shi da dukkan annabawa ) shine manzo na karshe da ALLAH ya aiko, shi kwa dan kabilar kuraishawa ne a cikin larabawa, dan haka da shi aka cika annabci; babu wani annabi bayan shi.
Alkur' ani shine kundi na Muslunci , dukkan wanda ya gaskata cewa daga Allah yake shi wannan al kur' ani, ya kuma yi  imani da shi gaba daya, to wannan ana kiran shi mumuni.
Imani ko da wannan ababe da suka gabata babu wanda ke ganin shi a cikin zuciyar mutane banda ALLAH; domin shi kadai ne ya san abin da zuciya ta kumsa, mutane sun san abinda ke zahiri ne kadai.
Domin haka ana dauka mutun musulmi idan ya yi firici da shahadar cewa babu wani abin bauta wanin ALLAH, kuma muhamad ( tsira da rahama ta musamman su tabbata a gare shi, shi da dukkan annabawa ) manzon ALLAH ne.
Idan ya firta wannan shahada lalle ya zama daya daga cikin musulmi, ya nada hakki kamar dukkan musulmi, haka kuma dukkan abin da ke hawan musulmi ya na hawan shi.
Wadannan abubuwa da ke rataya a kan shi abubuwa ne masu sauki, kuma ba masu yawa ba, daga cikin su:
1- sallah; zai yi ruku' u ga ALLAH so biyu da safe, wannan ruku' un kwa ganawa ce da ubangijin shi domin ya nemi rahama da tsarinshi daga dukkan sharri.
 Gabanin wannan ganawar zai yi alwala ( tsabtace gabban shi ), ko yayi wanka idan akoy janaba a tare da shi.
Sa' annan idan rana ta kau da tsakiya sai yayi raka' a hudu.
Idan kuma inuwar shi ta lunka tsayin shi so biyu sai ya yi raka' a hudu.
Ya kuma yi raka' a uku yayinda rana ta fadi.
Da dare zai cika sallolin shi da raka' a hudu.
Wannan sune salloli da ke wajibi a kan shi, ko wace daya daga cikin su bata wuce minti goma ba, ba' a kuma kayyade su da wani guri na musamman, ko wani mutun wanda dole za' a yi ta da shi, ba kuma wani tsani a cikin ta tsakanin mutun da ubangijin shi.
2- a cikin shekara akoy wani wata wanda musulmi yake azumta; a cikin wannan wata yana nisantar abinci da abin sha, ko saduwa tsakanin namiji da matar shi, daga safe har faduwar rana, wanan ko dan ya tsarkake zuciyar shi, ya kuma futar da tubin shi, ya kuma gyara halayan shi.
Sa' an nan wannan watan wata ne dake karantar da musulmi game da haduwa akan aikin al kheiri.
3- idan dukiyar musulmi ta haura bukatar shi da ta iyalin shi, ta kai wani haddi da shari' a ta kayyade, ta kuma shekara ba tare da ya bukace ta ba, ya na zama wajibi a kan shi ya fitarda wani kaso kankane  ( biyu da rabi cikin dari ), ya bayarda shi ga mabukata da talakkawa … abin da zai kawo hadin kai tsakanin al – ummah da rike juna.
4- Muslunci ya tanadarwa musulmi haduwa na lokaci zuwa lokaci; haduwa biyar a ko wace rana a lokacin sallah, inda suke dada jaddawa ubangijinsu bautar su da bukatuwarsu gare shi a tsayuwarsu gaban Shi; hakan kuma zai sa mai karfi a cikin su ya kasance ya na mai taimakawa wanda ba shi da karfi, masani ya sanar da wanda ba ya da sani, mawadaci ya taimakawa wanda ba shi da shi. 
Wannan salloli kwa ba su hana mutun gudanar da ayukan shi na yau da kullun, domin ba su daukar lokaci mai yawa.
Haka ne kuma Muslunci ya tanadar da haduwa ta mako a sallar ranar juma'a dake wajibi akan maza, wadda ita ma bat a daukar fiye da awa guda.
Bayan haka akoy haduwa so biyu a shekara a idin layya da na azumi, wadannan haduwa biyu ko halartar su ba wajibi ba ne ba, tare da cewa ko wace daya a cikin su ba ta daukar fiye da awa guda.
Sa' annan a karshe akoy haduwa ta shekara a guri na musamman, a lokaci kayyadadde.
Wannan haduwar wada ke farali ( dole ) so daya a rayuwar musulmi idan ya na da iko, hakika taro ne na karantarwa da fuskantarwa, tare da motsa jiki da kolluwa; wannan taro shine hajji.
Wadannan sune ibadodi da ke wajaba a kan musulmi a asali.
Yana kuma cikin ibada barin wasu ayukka kayyadaddu, wadanda kuma masu hankali na duniya sun hadu a kan cewa sharri ne, tamkar kisan kai   bad a hakki ba, ko ta' adi a kan dukiyar mutane, ko zalunci, ko giya, ko riba, ko karya, ko zina, ko karya, ko al gush, ko rishin da' a ga iyaye, ko rantsuwa a kan karya, ko shaidar zur, da abinda ya yi kama da haka na daga ababe munana wanda dukkan masu hankali sun san cewa sharri ne.
Idan musulmi ya gaza bayar da wasu daga cikin ababen da ke wajibi a kan shi, ko ya aikata wasu daga cikin ababen da aka hane shi, sa' an nan ya tuba, ya koma ga Allah , ya kuma nemi afuwa shi, ba sakka Allah zai masa afuwa, idan kuma bai tuba ba zai ci gaba da kasancewa cikin musulunci, tare da cewa shi mai sabo ne, wanda yake cancantar ukubar Ubangiji ta wani lokaci, ba kamar ta kafiri ba.
Musulmi zai iya samun kan shi a halin barin wasu hukunce hukunce na musulunci ba tare da ya yi inkarin daya daga cikinsu ba, wannan ko ba zai fitar da shi daga da' irar musulunci ba, face dai shi mai sabo ne.
Amma imani baya rarrabuwa, inda mutun zai yi imani da dukkan akidu na musulunci sa' an nan yayi inkarin akida guda zai kafirta.
Mutun zai iya kasancewa musulmi amma ba ya da imani, kamar wanda ya shiga cikin wata kungiya tare da cewa bai yarda da ka' idodin ta ba a hakika, kuma bai gamsu da ingancin ta ba, abin da ke da kwai shine kawai ya danganta kanshi gareta, domin leken asirin ta, ko bata ta.
Wannan kwa shi ne munafiki; wanda ke firta shahada da bakin shi, yake kuma aikata ayuka na Muslunci a zahira, tare da kunshe kafirci a cikin zuciyar shi, domin bai yi imani ba. Mutane suna masa hukuncin cewa shi musulmi ne; domin su ba su san abin da ke kumshe a cikin zukata ba.
Idan mutane suka yi imani da Allah, imani na hakika, suka kuma tsarkake Shi daga shirka ko tsani, tare da yin imani da mala' iku, da annabawa, da litattafai, da rayuwar lahira, da kuma kaddara, bayan firta shahada, suna kuma masu sallatar salloli na farilla, da azumtar watan Ramadan, suka kuma kasance suna masu fitar da zakka ta dukiyoyin su, da kuma aikin hajji da umra inda hali, tare da nisantar ababen da aka hane shi, to hakika wannan musulmi ne kuma mumini ne, zai kuma samu dandanon musulunci muddun ya rungumi hanyar musulunci da gaskiya.
Wannan hanyar kwa manzon tsira yayi muna bayaninta cikin kalimomi takaitattu wanda suka hada al khairi na duniya da lahira.
Wadannan kalimomi sune:  ya tuna a ko wane lokaci cewa Allah yana ganin shi, ya kuma san abin da zuciyar shi ta kunsa, dan haka kar ya saba mi Shi; saboda yana ganin shi, kar kuma ya fudda kauna soboda yana tare da shi, kar kuma ya samu kawaiti tare da cewa ya na ganawa da shi, kar kuma ya bukaci wani tare da cewa yana rokan Shi .
Idan ya saba masai ya komo zuwa gare Shi; domin mutun daman mai sabo ne, Ubangijin Shi kuma mai karbar tuba ne.
Wannan duka a cikin fadar manzon Allah yayin da ya ce: « kyautatawa shine: ka bautawa Allah kamar kana ganinshi, idan kai ba ka ganin Shi,  to, lalle Shi yana ganin ka ».
Wannan shine musulunci wanda ya zo da shari' a mai sauki, wadda mai ilimi da wanda ba shi da shi duka za su iya fahinta, ta kuma dace da kowa da kowa; ba ta dora wa kowa face abinda zai iya, tana tabbatar mishi da incin shi ba tare da sabawa Ubangijin shi ko cutar da wani ba.
Dan haka shi ne addini na jin kai da koncin hankali tare da salama.
Wannan shine addinin musulunci a takaice. 
An ciro wannan bahasi ne da ga littafin sheik: Ali Dandawi (Allah ya ji kan shi ) mai suna: kitab ta'arifun a'm bi dinil islam.