Adalci da gaskiyar sahabai ( Allah ya dada yarda da su )


   Allah ( ma daukaki ) Ya halicci aljani da mutun ba dan kome ba sai dan su bauta maSa, sai kuma Ya zabi wasu daga cikin bayin Sa wadanda sune manzannin Sa ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Su gaba daya ) ; Ya saukar da wahayin Sa agare su, Ya kuma umarce su da su isar da wannan wahayin zuwa ga bayin Sa; Allah yana cewa: «165. Manzanni mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kan Allah bãyan Manzannin. Kuma Allah yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima ». ( Suratun Nisa 165 ).

 

Sa' an nan kuma ya zabi manzo Muhammad ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) a cikin wadannan manzannin ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Su gaba daya ); Ya zabe Shi, kuma ya saukar da fiyayyen littafi, wanda ke shine  Alkur' ani a gare Shi, kamar yanda Ya sanya shari'ar Shi fiyayyar shari' o' i , sa' an nan Ya sanya tabewa ga wanda bai riki addinin da Ya zo da shi ba, wanda shine muslunci; Allah yana cewa: « 85. Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra ». ( Suratul Al-Imran 85 ).

 

Sa' an nan kuma manzon Allah Muhammad ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) ya karfafa wannan ma'anar yayin da ya ce:  "na rantse da wanda rai na ke hannun Sa, ba wanda zai ji labari na cikin wannan al ummar; bayahude ne ko crista, sa' an nan ya mutu ba tare da ya yi imani da abin da aka aiko ni da shi ba, face ya kasance cikin 'yan wuta". Muslim ne ya ruwaito wannan hadisin; hadisi mai number  153.

Saboda wannan manufar mai girma Allah ( ma daukaki ) ya kaddara ababe  da ke nuni ga hikmar Sa; daga cikin su:

1 -  Allah ya dauki alkawalin kiyaye Alkura' ni mai girma daga dukkan canji ( dadi ko kari ... ); Allah yana cewa:    « 9. Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato ( Alƙur'ãni ) , kuma lal1e Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi ». (  Suratul Al-Hijr 9 ).

2 – Allah ya zabi wasu mutane da suka cancanta domin su kasance sune sahabben nanzon Sa, Muhammad ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ), domin su dauki nauyin isar da addinin da manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) ya isar zuwa gare su; saboda addini ne na dukkan mutane da aljannu, ba tare da banbanci ba tsakanin fari da baki, ko balarabe da wanda ba balarabe ba; Allah yana cewa: « 28. Kuma ba Mu aika ka ba fãce zuwa ga mutãne gabã ɗaya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba ». ( Suratul Saba ).

 

Abdullahi dan Mas' udu ( Allah ya dada yarda da shi ) yana cewa: "Allah ya diba zukata sai ya samu zuciyar  Muhammad ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) ita ce mafi kyawon zukatan bayin Sa, sai ya zabe Shi, Ya kuma zabe Shi ga manzonci, sa' an nan Ya diba sauran zukata sai Ya samu zukatan sahabben manzon Allah sune fiyayyen zukata sai Ya zabe su dan su kasance sune abokanen manzon Shi, wadanda ke bada rayukkan su domin daukaka addinin Allah".

 

Ya kai dan uwa ga yanda mijin Fatimatu Zahra, ma'aifin jikokin manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ), shugabanin samarin aljanna, Ali dan Abu talib ( Allah ya kara yarda da Shi ) , ya sifanta sahaben manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi kuma ya yarda da sahabbai duka); abu Araka ya ce: "na yi sallar asubahi bayan Aliyu dan abu talib  ( Allah ya kara yarda da Shi ), bayan ya yi sallama sai ya juyo ta hannun dammar shi yana da kamar damuwa, bayan rana ta bullo ta kuma bayyana a kan bangon masallaci ya yi raka'a biyu, kuma ya jujjuya hannayen shi yana mai cewa: wallahi naga sahabben manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) kuma ban ga abin da ya yi kama da su ba !! suna kasancewa da safiya masu kura da alama a goshi saboda sun tafiyar da daren su a cikin sallah da karatun Alkura' ni, idan aka tunatar da su da Allah sai ka ga tufafin su suna jikewa da hawayen su, wallahi kai ka ce: sun kwana cikin rabkanuwa ne da sabon Allah !!".

Rayuwar manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) ta fara a Makkah, yayin da wasu mutane wadanda ba su da yawa suka yi imani da Shi, sai ya kasance an kalubalance su da kuntatawa da kuma muzgunawa iri iri daga kuraishawa, duk da haka suka yi hakuri su ka kuma jure tare da manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) , suna ma su kira zuwa ga addinin Allah da hikma; abin da ya sa wasu suka ci gaba da muslunta a cikin Makkah; a nan za mu ga gaskiyar imanin al muhajirin ( wadanda suka muslunta a Makkah ), wadanda suka sanya rayukan su da dukiyoyin su ba dan kome ba sai dan taimakawa addinin Allah, kuma suka baro dukiyoyin su da 'yan uwan su da abokanen arzikin su, suka yi hijira tare da manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) zuwa Madina !!

Me nene ya sanya su suka yi duk haka ?!

Shin tsoron manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) - wanda Shima yake tare rauni - ne ya sanya su suka yi haka ?!

Ko kuma kodan abin da ke tare da shi na dukiya ko matsayi ne ya sa su suka aikata hakan ?!

Amsar ita ce: ba wannan ko wancen ba ne ya sanya su suka aikata hakan, abin da ya sanya su suka yi haka shine karfin imani.

Lalle munafirci, wanda ke shine bayyana imani tare da boye kafirci, babu sababin shi a  Makkah ; domin muslunci ba shi da karfin da za'a ji tsoron shi, kamar yanda babu wata dukiya da za'a yi kodan samu a cikin shi. Dan haka munafirci bai kasance ba a Makkah a cikin sahaben manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ).

Yanzu tanbaya mai muhimmanci ita ce:

Shin al muhajirin wadanda sifofin su suka gabata zamu dauke su adilai ko kuma a'a ?

Kuma kaka zamu yi da abin da suka isar gare mu wanda  ke shine bangare na addini ?

Shin za mu karbi abin da suka isar zuwa gare mu na addini ko kuma zamu mayar da shi ne ?

Amsar da babu mumini da ke da shakku a kanta ita ce: alkura' ni wanda ke maganar Allah ne ya zo da yabon su, tare da tabbatar da cewa sun samu gabaci a cikin wannan addinin, kuma falalar su tana da yawa.

Allah madaukaki yana cewa a cikin Alkura' ni : « 100. Kuma mãsu tsẽrẽwa na farko daga Muhãjirina da Ansar da waɗanda suka bi su da kyautatãwa, Allah Ya yarda daga gare su su kuma sun yarda daga gare Shi, kuma Ya yi mãsu tattalin gidãjen Aljanna; Ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, suna madawwamã a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma». ( suratut tauba 100 ).

 

Kuma allah yana cewa: « 218. Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka yi hijira kuma suka yi jihãdi a cikin hanyar Allah waɗannan suna fãtar ( sãmun ) rahamar Allah kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai ». ( suratul baqara 218).

Kuma wadanda suka yi imani da annabcin manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) suna tabbatar da adalcin su, domin ya yabe su so da yawa, kamar yayin da Ya ce: "lalle talakawan almuhajirin za su rigayi masu dukiya a cikin su zuwa Aljanna da shekara arba'in".

Shaida da Aljanna ba ta samuwa ga wanda ba adili, mai cikekken imani ba.

Wanda bai karbi yabon Allah ga almuhajirin ba, kuma bai yarda da adalcin su ba, na wa zai karba ?.

Kuma da me nene zai baiwa musulmi amsa game da ayoyin da suka zo a kan yabon su ?

Bayan musulmin nan sun yi hijira tare da annabi ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) zuwa Madina sun samu kyakyawon tarye daga 'yan uwan su al – ansar (mutanen Madina ), kuma mutanen nan na Madina sun bada kyakyawan misali abin rubutawa da zinariya, wanda tarihi ba zai taba mantawa ba !!!

Me nene kodan su na duniya wajen mutanen da aka koro, ana neman kashe Shi, shi da sahabben Shi ?

Hasali ma mubaya'ar da suka yi maSa ta kasance cikin cikekken sirri da tsoro mai yawa.

Ga ababe guda biyu game da mubaya'ar nan:

Na farko: amincewar Abbas dan Abdul muttalib ( Allah ya kara yarda da Shi ) da al – ansar tana bayyana karara, yayin da ya tunatar da su da matsayi da hakkin dan dan uwan sa; manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ); yana mai cewa: ya ku jama'ar khazraj: kun san matsayin manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) a gun mu, mun kare Shi daga mutanen mu wadanda sun san matsayin Sa domin Shi mai daukaka ne cikin su, Ya kuma ki kome banda komawa wajen ku, idan kun san za ku iya kare Shi da cika alkawullan da ku ka yi, to ga Shi nan zuwa gare ku, tare da sanin cewa Shi fa yana cikin daukaka da kariya a cikin jama'ar shi da garin shi. Sai al ansar suka ce: mun ji abin da ka fada, ka yi magana ya manzon Allah; ka nemi dukkan abin da kake so wajen mu, sai manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) ya karanta Alkura' ni mai tsarki, ya kuma yi kira zuwa ga Allah, tare da kodaitarwa ga muslunci, sa'an nan ya ce: ina yi muku mubaya'a akan ku kare Ni daga abin da kuke kare matan ku da "ya"yan ku.

Shin zai taba yiwa Abbas ( Allah ya kara masa yarda ) ya mika dan dan uwan Shi ga mutanen da bai yarda da adalcin su ba ?!

Abu na biyu shine: girman nauyin da al ansar suka dora ma kan su da sakamakon wannan mubaya'a; As' ad dan zurara ( Allah ya kara masa yarda ) - wanda ke shine karami daga cikin mutane saba'in na al ansar – ya ce: sannu sannu ya ku mutanen Madina, wallahi ba mu zo wajen Shi ba sai dan mun tabbatar da cewa manzon Allah ne, kuma karbar Shi rabuwa da larabawa gaba daya ne, kuma kisan fiyayyun ku ne; kuna da dayan zabi biyu: ko dai ku yi hakuri akan haka Allah Ya sakauta muku, ko kuma idan kuna jin tsoro ku yi bayani dan a karbi uzurin ku, sai suka ce: kau da hannun ka ya kai As' ad, wallahi ba za mu warware wannan mubaya'a ba har abada.

Rabuwar su da kabilun da ke tare da su a Madina, musamman yahudawa, zai jefa su a cikin hadarin halakar da su gaba daya !

Dan haka sabubba na munafirci babu su a farkon kasancewar manzon Allah  ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) a Madina; domin musulmi su ke da rauni.

Ga daya daga cikin ababen da za su nuna maka hakan: yayin da manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) ya zo Madina an ce da shi: da ka je ka gaida Abdullahi dan Ubayi, sai manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) ya hau jaki, yana tare da sahabben Sa, ya je ya iske Abdullahi dan Ubayi, yayin da ya isa sai Abdullahi ya ce da shi: ka tsutar da mu da warin jakin ka, sai wani daga cikin sahabbai ya ce: wallahi iskan jakin manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi )  ya fi iskan ka. Sai wani daga cikin mutanen da ke tare Abullahi dan Ubayi ya zage shi, sai fada ya kabre tsakanin bangarorin biyu.

Allah ya daukaka addinin Sa  yayin da ya shiryar da manya manya mutanen Madina da kuma shigar da ma fi yawan mutane a cikin sa, abin da ya kai ga baiwa musulmi nasara akan kafirai a yakin badr.

A wannan lokacin sai wasu daga cikin mutanen Madina suka bayyanar da shiga cikin muslunci tare da boye kafircin su saboda cima wasu manufofin su na duniya. Abdullahi dan ubayi dan salul ya ce wa mushirikai da masu bautar gumaka: wannan addinin ya samu karfi, ku shige shi, sai suka bayyana musluncin su; daga nan sai munafirci ya fara.

Adadin sahabbai ya ci gaba da karuwa, kuma mutane su kai ta shiga cikin wannan addinin bayan bude Makkah, har ma adadin musulmin da suka yi hajji tare da manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) ya kai kamar dubu dari.

Idan muka yi gini a kan abin da ya gabata abu kamar haka zai bayyana a gare mu:

1 – kiran mutun sahabi yana da ma'ana mai fadi kamar yanda yake da ma'ana takaitacce. Ma'anar shi mai fadi ita ce: sahabi shine duk wanda ya ga manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) kuma ya yi imani da Shi; dan haka akwai fifiko tsakanin sahabbai: misali Abdurrahmane dan Auf ( Allah ya kara masa yarda ) da wadanda suka yi rigaye zuwa ga muslunci, suka muslunta kafin sulhun hudaibiyya, suka kuma ciyar, sun fi wadanda ba su muslunta ba kuma ba su ciyar da dukiyoyin su ba sai bayan wannan sulhun kamar Khalid dan Walid ( Allah ya kara musu gaba dayan su yarda ).

Allah yana cewa: « 10. Kuma me ya sãme ku, bã zã ku ciyar ba dõmin ɗaukaka kalmar Allah, alhãli kuwa gãdon sammai da ƙasã na Allah ne? Wanda ya ciyar a gabãnin cin nasara, kuma ya yi yãƙi daga cikinku, bã ya zama daidai ( da wanda bai yi haka ba ) . waɗancan ne mafĩfĩta girman daraja bisa ga waɗanda suka ciyar daga bãya kuma suka yi yãƙi. Kuma dukansu Allah Ya yi musu wa'adi da ( sakamako ) mai kyau, kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa ». ( suratul al hadid 10).

Wadanda suka abokance Shi kafin cin Makkah da yaki sun kebanta da wata falala wadda wadanda suka abokance Shi bayan haka ba su samu ba; dan haka ya ce da Khalid dan Walid         ( Allah ya kara masa yarda ): "kad ku zagi sahabbai na" domin sun abokance Shi kafin Khalid da wadanda suka yi imani da shi daga baya su abokance shi.

 

Ga wani misali kuma wanda ya fi futowa fili: Abubakr siddik ( Allah ya kara masa yarda ) wanda shine ya fi dukkan sahabbai falala ( Allah ya kara musu yarda gaba dayan su ), wannan kwa da abin da ya kebanta da shi koma bayan su; manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) yana cewa: "lalle ba bu wanni wanda ke da falalar taimaka mini da ran shi da kuma dukiyar shi kamar Abubakr dan Abu kuhafa, inda zan riki wani abin so, so na musamman, da ya kasance Abubakr ne, amma soyayya ta muslunci ta fi, ku rife mini dukkan kofofi da ke zuwa ga masallaci banda kofar Abubakr".

 

Kuma manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) ya ce yana mai bayyana falalar Abubakr: "Allah ya aiko Ni sai ku ka ce: ka yi karya, sai Abubakr ya ce: ka yi gaskiya, ya kuma taimaka mini da ran shi da dukiyar shi. Shin za ku bar mini aboki na ?". a nan gurin Ya kebe shi da abokantaka kamar yanda Alkura' ni ya kebe shi da abokantaka a cikin fadar Allah ma daukaki: « 40. Idan ba ku taimake shi ba, to, lalle ne Allah Yã taimake shi, a lõkacin da waɗanda suka kãfirta suka fitar da shi, Yanã na biyun biyu, a lõkacin da suke cikin kõgon dũtse, a lõkacin da yake cẽwa da sãhibinsa: Kada ka yi baƙin ciki, lalle ne Allah Yanã tãre da mu. » ( suratul al taubah 40 ).

Umar dan khaddab kwa manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) ya nuna mana falalar Sa yayin da ya ce: "Allah ya sanya gaskiya a kan harshen Umar da zuciyar shi !", kuma manzon Allah ( tsira da amicin Allah su tabbata a gare Shi ) ya ce da shi: "na rantse da wanda rai na ya ke hannun Shi, shaidan bai taba ganin ka akan wata hanya ba face ya sake wata hanyar".

Kuma Umar haka ma Abubakr ba su taba shugabantar da wani munafiki, ko wani dan uwan su akan musulmi ba.

Kuma sahabbai sun tabbatar da wannan fifikon tsakanin su; imam Ahmad ya ruwaito a cikin littafin shi "al musnad" daga Wahab dan suwa' i yana mai cewa: " Aliyu dan abu talib ( Allah ya kara ma dukkan sahabbai yarda ) ya yi mana huduba, a cikin wannan hudubar ya ce: wanene fiyeyyen wannan al ummar bayan manzon ta ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) ? sai na ce: kai ya shugaban muminai, sai ya ce: A'a, fiyayyen wannan al ummar bayan annabin ta shine Abubakr, sa' an nan Umar Allah ya yarda da su".

Tare da wannan fifikon muna tabbar da cewa su dukkan su adilai ne, masu gaskiya.

2 – al muhajirin babu a cikin su wanda aka tuhuma da munafirci.

3 – al ansar har yakin badar babu wanda aka tuhuma da munafirci a cikin su.

4 – munafirci ya bayyana ne bayan yakin badar a wajen wasu mutanen a Madina; domin shugabannin su sun shiga muslunci, haka ma ma fi yawan mutane; sai suka bayyana muslunci tare da boye kafirci; saboda muslunci ya kasance shi ne mai karfi da fada a ji.

5 – wadanda su kayi rigaye zuwa ga muslunci daga cikin al muhajirin da al ansar, da wadanda su ka muslunta bayan bude Makkah, adalcin su da gaskiyar su sun bayyana ne ta hanyoyi kamar haka:

A – yabon da Allah Ya yi musu a cikin Alkura' ni; Allah yana cewa  : « 100. Kuma mãsu tsẽrẽwa na farko daga Muhãjirina da Ansar da waɗanda suka bi su da kyautatãwa, Allah Ya yarda daga gare su su kuma sun yarda daga gare Shi, kuma Ya yi mãsu tattalin gidãjen Aljanna; Ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, suna madawwamã a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma ». ( suratut tauba 100 ).

B – yabon da manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) Ya yi musu kamar a cikin fadar Shi: "kad ku zagi sahabbai na, inda dayan ku zai ciyar da tamkar dutsen uhudu na zinariya bai kai muddu ko rabin muddu na dayan su ba", da fadar shi "fiyayyen karni shine karnin da nake cikin shi, sa' an nan wanda zai biyo shi,  sa' an nan wanda zai biyo shi"

C – kasancewar wadanda suka yi rigaye ga addinin muslunci sun yi wa wadanda suka biyo bayan su shaida a kan cewa su adilai ne kuma masu gaskiya ne.

D – jama'ar sahabbai jama'a ce wadda ta san sharri da makircin da munafukai ke kitsa musu; saboda Allah Ya umarce su da su  yi takatsantsa da munafikai; Allah yana cewa: « sai ka yi saunarsu. » ( suratut Munãfiƙũn 4 ). Kuma ya taimaka musu akan hakan kamar yanda Alkura' ni yake sifanta munafikai, har inda munafikan ma suke ji tsoro; Allah yana cewa: « 64. Munãfukai sunã tsõron a saukar da wata sũra a kansu,wadda take bã su lãbãri ga abin da yake cikin zukãtansu. Ka ce: Ku yi izgili. Lalle ne, Allah ne Mai fitai da abin da kuke tsõro ». ( suratut Al-Taubah 64 ).  

Yana daga cikin abin da ya zo a cikin Alkura' ni game da sifofin munafikai fadar Allah: « 30. Kuma dã Munã so, dã lalle Mun nũna maka su. To, lalle kanã sanin su game da alãmarsu. Kuma lalle kanã sanin su ga shaguɓen magana, alhali kuwa Allah Yanã sanin ayyukanku ». ( suratul Muhammad ). Kuma Alkura' ni Ya kara bayani game da sifofin su yayin da ya ce: « 142. Lalle ne munãfukai sunã yaudarẽwa da Allah, alhãli kuwa Shi ne mai yaudarasu; kuma idan sun tãshi zuwa ga salla, sai su tãshi sunã mãsu kasãla. Suna nũnawa mutãne, kuma ba su ambatar Allah sai kaɗan ». ( suratul Al- Nisa).

Alkura' ni so da yawa ya yi bayani game da su a cikin al amurra masu yawa yana mai fadin   sifofin su ba tare da ya fadi sunayen su ba; lalle kwa siffofi na munafikai da alkura' ni ya yi bayani game da su suna maimaituwa a ko wane zamani; dan haka muminai sai su kiyaye kad su siffanta da su, kuma su kiyayi sharrin wanda ya siffanta da su.

Hakika manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) ya sanya son al ansar alama ce ta imani, kin su kuma alama ce ta munafurci, Ya kuma fada wa Huzaifa dan Yamane    ( Allah ya kara ma dukkan sahabbai yarda )  sunayen munafukai; dan haka Umar da sahabbai ba sa sallatar gawar wanda Huzaifa bai sallata ba.

Zan takaita game da abin da ke nunin cewa sahabbai sun san sifofi da wasu daga cikin munafukai akan kissosi guda biyu kawai: 

1 – kissa ta farko ta abku akan Abdullahi dan ubayi dan salul, shugaban munafukai, bayan ya sullube daga bataliyar musulmi lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa yakar mushirikai a yakin Uhudu, bayan haka sai ya tashi wata ranar juma'a –kamar yanda ya kasance yana aikatawa duk juma'a bayan  manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) ya gama huduba  ya tashi yana mai cewa: ya ku jama'a wannan manzon Allah ne ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) a cikin ku, Allah Ya daukaka ku Ya kuma girmama ku da shi, ku taimaka maSa, ku kuma kama maSa, ku saurara maSa kuma ku yi maSa da'a- bayan ya fadi haka sai musulmi suka kama rigar shi, suka ce da shi: zauna ya kai mikiyin Allah, kai ba ka cancanci fadar haka ba bayan ka aikata abin da ka aikata, sai ya futo yana mai tsallaka mutane yana cewa: tamkar wani sharri na fada.

Kissa ta biyu kwa: kissar sallar manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) a gidan Malik dan dakhsham ( Allah kara masa yarda ) bayan ya nemi hakan ga manzon Allah         ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) domin ya rika sallah a gurin; saboda ganin shi ya raunana; sai sahabbai suka kasance suna magana a kan munafurci da munafukai.

Imam Annawawi ya ce - yana mai bayani akan wannan hadisin da ke cikin ingantaccen littafin Muslim -: "sun tantauna batun munafukai da irin ayukkan su munana, da sharrin da yake samun su daga wadannan munafukan".

E – cewa Aliyu dan abu talib da alaye ( Allah kara masu yarda ) bai inganta ba cewa sun tuhumi sahabbai game da adalci ko gaskiyar su ba, hasali ma sun rayu tare su suna ma su so da kaunar  juna.

F – son alayen gidan manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) shine abin da sahabbai suka ruwaito mana, shin sakamakon su zai kasance bayan haka wajen wadanda ke da'awar son alayen manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) shine kin wadannan sahaben ?!!!

G – kaka wanda ba adili ba zai samu wannan dacewar da kowa yake gani ?! kuma kaka zukatan su suka hadu akan wannan addinin tun zamanin manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) har bayan mutuwar Shi ?!!! dan me ba su bar addinin ba bayan mutuwar manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) ba ?!!

Kuma mu tambayi kanun mu: shin sabanin da ya samu tsakanin sahabbai ( Allah Ya yarda da su duka ) zai iya kasancewa sababin shakka akan adalci da gaskiyar su ?

Amsa ita ce: malamai sun hadu a kan kariya daga aikata zunubi game da annabawa da manzanni ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Su ), bayan su ba bu wani mai irin wannan kariyar komin matsayin sa; dan haka sahabbai da shahidai da mutane nagari suna kuskure, kuma idan sun tuba Allah yana karbar tubar su, kamar yanda Yake gafarta masu da kyawawan ayukkan su, ko kuma jarrabawa da Allah Yake musu. Kuma ba shakka sahabai sun kaddamar da ayukka ma su yawa  dan ci gaban muslunci kamar jihadi da abin da ya yi kama da haka.

Wannan idan ya kasance sun aikata kuskuren da gangan ne, amman idan ya kasance sun yi kuskure ne a kan ijtihadi; suna tsammani suna kan gaskiya, lalle wanda ya samu gaskiya yanada lada biyu, wanda kuma ya yi kuskure yanada lada daya.

 

Wannan shine abin da za mu fada game da abin da ya kasance tsakanin sahabbai na sabani, tare da cewa sahabbai da yawa ba su shiga cikin wannan fitinar ba.

Shin yana cikin adalci cewa dukkan wanda ya yi kuskure mai laifi da zunubi ne ? sa' an nan a sabkar da wannan hukuncin akan sahabbai, game da abin da ya faru tsakanin su, bayan haka ya kasance dalili ne na cewa su ba adilai ne ba, kuma ba ma su gaskiya ba ne ba, kuma a musu hukuncin kafirci ko munafirci ?!

Lalle Alkura' ni ya yi bayani a kan yaki tsakanin muminai yayin da ya ce: « 9. Kuma idan jama'a biyu ta mũminai suka yi yãki, to, kuyi sulhu, a tsakãninsu. Sai idan ɗayansu ta yi zãlunci a kan gudar, to, sai ku yãƙi wadda ke yin zãlunci har ta kõma, zuwa ga umurnin Allah. To, idan ta kõma, sai ku yi sulhu a tsakãninsu da ãdalci kuma ku daidaita. Lalle Allah na son mãsu daidaitãwa. 
10. Mũminai 'yan'uwan jũna kawai ne, sabõda haka ku yi sulhu a tsakãnin 'yan'uwanku biyu, kuma ku bi Allah da taƙawa tsammãninku, a yi muku rahama ». ( suratul Al - hujurat ); a cikin wannan ayar Alllah Ya sifanta dukkan bangarorin da imani tare da cewa sun yaki junan su kuma wani bangare ya zalunci wani bangare.

Kuma manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) ya ce game da Al Hasan: "lalle wannan da na ne, kuma Allah zai hada kanun bangarori masu girma biyu na musulmi da ke yaki da juna da Shi"  Ya ambaci bangarorin biyu  masu yakin juna da cewa musulmi ne.

Ba dukkan abin da ke zalunci da sabani ke kore imani ba, kuma ba ya halittar da la'anta; kaka kuma idan wannan ya kasance ne daga sahabban manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) wadanda su ne fiyayyen karni !!!

A karshe:

 

Lalle ahlus sunna suna da kudurin cewa sahabbai dukkan su adilai ne, kuma bai halitta a soki daya daga cikin su ba, tare da kore ganin cewa suna da kariya daga aikata sabo ko kuskure, kuma adalcin su yana tare da karfin imanin su ne, wanda ba ya basu dammar yiwa manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) karya.

Muna cewa ga dukkan wanda ke zagin sahabbai, ko zargin su da munafirci ko kafirci:

Shin ba ka gamsu da yabon da Allah ya yi akan su ba ?-

- Shin ba ka yarda da yabon da manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi )  ya yi musu ba ? kuma ba ka yarda da wasicin da ya yi game da su ba ?

- shin yabon da Ali  ( Allah ya kara yarda da shi ) yake yi musu ba ya tasiri akan ka ?

Ina son ka yi tunani da hankalin ka game da dukkan abin da ka ji a kan su na zargi ko suka, ba tare da ka tasirantu da wani abu ba. Kuma ka yi tunani mai zurfi game da:

1 – cewa munafiki mai bayyana imani tare da boye kafirci ba zai isar da addinin da ya ke ki ba, kuma ba zai karantar da shi ba.

2 – Allah ya dau nauyin kiyaye addinin Ss, shin zai wakilta munafukai wajen isar da shi ? ba zai taba yiwa ba; wannan dukkan mai hankali ya san da cewa haka ba zai yiwu ba, kaka kuma daga Allah madaukaki ?

3 – mu kaddara cewa wani daga cikin munafikai ya ruwaito wani hadisi, idan ya yi daidai da  Alkura' ni ko kuma ya yi daidai da abin da sauran mutane suka ruwaito kenan ya dace da gaskiya, idan kwa ya saba babu shakkar cewa ba gaskiya ne ba.

Babar tambaya da za mu rife da ita ita ce:

Lalle mu mun yi imani da cewa manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) gaskiya ne, da kuma cewa Alkura' ni gaskiya ne, kuma wadanda suka isar da Alkura' ni da sunnar manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) sune sahabbai ( Allah kara yarda da su gaba daya ); shin kuna son ku fallasar da shaidun mu ne dan ku ce: Alkura' ni da sunna ba gaskiya ne ba ?!

 

Ina neman tsarin Allah daga shaidan abin jifa:

« 29. Muhammadu Manron Allah ne. Kuma waɗannan da ke tãre da shi mãsu tsanani ne a kan kãfirai, mãsu rahama ne a tsakãninsu, kanã ganin su sunã mãsu rukũ'i mãsu sujada, sunã nẽman falala  daga Ubangijinsu, da yardarSa. Alãmarsu tanã a cikin fuskõkinsu, daga kufan sujuda. Wannan shĩ ne siffarsu a cikin Attaura. Kuma siffarsu,a cikin Injĩla ita ce kamar tsiron shũka wanda ya fitar da rẽshensa, sa'an nan ya ƙarfafa shi, ya yi kauri, sa'an nan ya daidaita a kan ƙafãfunsa, yanã bãyar da sha'awa ga mãsu shũkar' dõmin ( Allah ) Ya fusãtar da kãfirai game da su. Kuma Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga cikinsu, da gãfara da ijãra mai girma ». ( suratul Al – fath 29 ).