buwayar Alkura' ni a cikin shari'ar Sa mai girma


Da sunan Allah mai rahama, mai jin kai

buwayar Alkura' ni a cikin shari'ar Sa mai girma

 

Alkur'a' ni yana shiryarda mutun zuwa ga abin da ke kaiwa ga dadin kai da daukaka.

Babban abin da ke jan hankalin mutun da himmar shi shi ne: son da musulmi suke yiwa Alkura' ni, da imanin su wanda babu wata shakka a kan cewa daga Allah Yake.

 

1 - Ina fuskokin buwaya a cikin Alkura' ni ?

2 - Me kuma yasa mutane suke karbar Shi da sauki ?

3 - Me nene sababin da ya sa masu imani da Shi a ko wane lokaci suke karuwa, musamman ma a wannan zamanin namu ?

 

Amsa ga wadannan tambayoyi tana tare da sanin fuskokin buwayar Alkura' ni, wadanda suke masu yawa, hasali ma ya na daga fuskokin buwayar Shi kasancewar mutane ba su iya kewayo da wadannan fuskoki.

Za mu takaita a kan fuska wadda tafi muhimmanci da daukaka; ita ce: shari'ar da Alkura' ni ya zo da ita wadda ke ta kai matuka wajen kyau a cikin hukunce hukuncen ta.

Wannan shari'ar ta banbanta da kasancewar ta mai sauki, da adalci, da game dukkan bangarorin rayuwa, tare da baiwa kome hakkin sa, tana tabbatar wa kowa rayuwa ta dadin kai da duk dan Adam yake nema, wannan kuma shi ne ya sa mutane suke son Alkura' ni kuma su ke imani da Shi. Tare da cewa sun san cewa maganar Allah ne wanda Ya san abin da ke gyara mutane a ko wane zamani da ko wane guri.

Alkura' ni Ya kasance da wadannan sifofi a wajen musulmi; littafi ne mai kunshe da rahma da shirya da haske ga wanda ya yi imani da Shi.

Shari'ar da Alkura' ni Ya zo da ita ta banbanta da wasu abubuwa da dukkan dan Adam yake bege; daga cikin ababen da wannan shari'a ta kebanta da su akwai:

1 – adalci da rishin cin zali

Alkura' ni Ya yi umarni da adalci, wannan kwa yana bayyana a cikin umarnin da Alkura' ni ya yi da adalci a cikin shaida ko da kwa akan shi mai shaidar ne, kuma kad ya ji nauyi a cikin shaida, ba tare da banbanci ba tsakanin mai arziki da talakka, haka ma tsakanin na kusa da na nesa, hori ko baki.

Allah madaukaki Ya ce a cikin Alkura' ni mai girma:  { 135. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayuwa da ãdalci, mãsu shaida  sabõda Allah, kuma kõ dã a kanku ne kõ kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko ( wanda ake yi wa shaida kõ a kansa ) ya kasance mawadãci kõ matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al'amarinsu. Sabõda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kõ kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Yã kasance Masani ga abin da kuke aikatãwa } [ Suratul Al-Nisa ].

Hasali ma Alkura' ni Ya yi umarni da adalci koda ana tsoran abkuwar khusuma.

Allah madaukaki Ya ce a cikin Alkura' ni mai girma: { 8. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayin daka dõmin Allah mãsu shaida da ãdalci. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutane ta ɗauke ku a kan bã zã ku yi ãdalci ba. Ku yi ãdalci Shĩ ne mafi kusa ga taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa }. [ Suratul Al-Ma'idah ].

1 – yana daga buwayar Alkura' ni kasancewar Shi ya hana zalunci;

Allah madaukaki Ya ce a cikin Alkura' ni mai girma: { kuma wanda ya yi zãlunci a cikinku zã Mu ɗanɗana masa azãba mai girma }. [ Suratul Al-Furqan 19 ].

Allah madaukaki Yana kuma cewa a cikin Alkura' ni mai girma: { Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa }  [Suratul Al-Shu'ara 227 ].

Allah madaukaki Ya ce a cikin Alkura' ni : { To, bone yã tabbata ga waɗanda suka yi zãlunci daga azãbar yini mai raɗaɗi! } [ Suratul Zukhruf 65 ].

Hasali ma ya zo a cikin Alkura' ni cewa mutun kad ya zalunci koda kan shi ne;

Allah madaukaki Yana cewa a cikin Alkura' ni: { Kuma wanda ya aikata cũta kõ kuwa ya zãlunci kansa, sa'an nan kuma ya nẽmi Allah gãfara, zai sãmi Allah Mai gãfara, Mai jin ƙai }. [ Suratul Al-Nisa 110 ].

Allah madaukaki Yana kuma cewa a cikin Alkura' ni: { Lalle ne Allah ba Ya zãluntar mutãne da kõme, amma mutãnen ne ke zãluntar kansu } [ Suratul Yunus 44 ].

Kai ya ma zo a cikin Alkura' ni cewa Allah ba Ya son zalunci;

Allah madaukaki Yana cewa a cikin Alkura' ni: { Kuma Ubangijinka bã Ya zãluntar kõwa } [ Suratul Al-Kahf 49 ].

Allah madaukaki Yana kuma cewa: { Kuma Allah bã Ya nufin zãlunci ga bãyinSa } [Suratul Gafir 31 ].

Dan haka hukunce hukunce da Alkura' ni ya zo da su sun kasance mu'ajiza ne domin sun hana zalunci a kan kowa, musamman ma a kan mata, dan haka ya hana mijin ta ma ya ci zalin ta;

Allah madaukaki Ya ce a cikin Alkura' ni: { Kuma sũ mãtan suna da kamar abin da yake a kansu, yadda aka sani } [ Suratul Al-Baqarah 228 ].

Alkura' ni Ya zo da dukkan abin da ke girmama mace; ya kiyaye hakin ta a matsayin ta na 'yar uwa, ko uwa, ko mata, wannan kwa a cikin halin aure, ko saki, ko shayarwa, ko gado da sauran su.

Wannan kwa ya kayatar da mata masu yawa a cikin tarihi, abin da ya sa da yawa suka muslunta, kuma su ka yi imani da cewa Shi wannan Alkura' ni yana da mu'ajiza a cikin hukunce hukuncen sa, soboda ya aje mace a matsayin ta da ya dace da ita.

3 – yana kuma daga cikin ababen da suka sa mutane suke son hukunce hukuncen muslunci kasancewar su suna kare hakkin dan Adam.

hukunce hukuncen muslunci sun samar wa 'yan Adam koncin hankali game da rayon su da jinin su da dukiyoyin su, da iyalen su, da hankullan su, da incin su.

Allah madaukaki Yana cewa a cikin Alkura' ni: { 29. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci dũkiyõyinku a tsakãninku da yaudara, fãce idan ya kasance, daga fatauci ne, bisa yardatayya daga gare ku. Kuma kada ku kashe kãnku. Lalle ne Allah Yã kasance, game da ku, Mai jin ƙai ne } [ Suratul Al-Nisa ].

Allah madaukaki Yana kuma cewa : {188. Kada ku ci dukiyõyinku a tsakãninku da ƙarya, kuma ku sãdu da ita zuwa ga mahukunta dõmin ku ci wani yanki daga dũkiyõyin mutãne da zunubi alhãli kuwa kũ, kuna sane }. [ Suratul Al-Baqarah ].

Allah madaukaki Yana kuma cewa : { 256. Bãbu tĩlastãwa a cikin addini} [ Suratul Al-Baqarah ].

Allah madaukaki Yana kuma cewa : { kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba } [ Suratul Qaf 45 ].

Inda dukkan jama'a na duniya za su yi aiki da dokokin da muslunci ya zo da su, da za su yi mamakin sakamako da za su samu a bangaren koncin hankali, da rage kashe kashe, da sata da ta'adanci da makamantan haka, kuma da sun san cewa wannan shari' ar mu'ajiza ce a cikin hukunce hukuncen ta.

Kuma dukkan hukunce hukuncen muslunci sun zo ne dan samar da maslaha ta dan Adam, da kuma kare shi daga dukkan sharri.

Misali:

-  Alkura' ni Ya haramta giya saboda tana gusar da hankali, sai ya tsutar da jama'a kuma ya tsutar da kansa, wannan kwa bayan tsutar da lafiyar sa.

- Ya kuma haramta naman alade wanda ilmi na zamani ya tabbatar da cutarwar shi ga lafiyar wanda yake cin shi; a cikin naman shi a kwai wani shinadarin "bolik" wanda jike ba ya iya fitar da fiye da 2% ta hanyar fitsari; saboda haka ne mai cin naman alade yake fama da ciwan gabbai, kuma a cikin jikin sa a kwai wasu tsutsotsi masu hadarin gaske, idan suka kai ga kwokwalwa suna sabbaba hauka, kama yanda suke sabbaba makabta idan suka kai ga idanu … da illoli masu yawan gaske.

4 – daga cikin ababen da suka sanya mutane suke karban wannan Alkura' nin akwai sauki wajen fahimtarsa kamar yanda ya ke da sauki wajen aiki da abin da ke cikin Sa.

Allah madaukaki Yana cewa a cikin Alkura' ni : { 17. Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa? }  [ Suratul Al-Qamar 17].

Allah madaukaki Yana kuma cewa: { Allah bã Ya nufi dõmin Ya sanya wani ƙunci a kanku, kuma amma Yanã nufi dõmin Ya cika ni'imarSa a kanku, tsammãninku kunã gõdewa }  [Suratul Al-Ma'idah 6 ].

Hukunce hukuncen muslunci mu'ajiza ne; domin ba  su kallafa mutun abin da ba zai iya ba; Allah madaukaki Yana cewa a cikin Alkura' ni : { 286. Allah ba Ya kallafa wa rai fãce ikon yinsa } [ Suratul Al-Baqarah ].

Bayan haka kuma yana daga saukin shari' ar da Alkura' ni Ya zo da ita kasancewar ta kunshi abin da ake cewa ( rongome ), ma'ana saukakewa dan Adam dukkan abin da ya fi karfin sa; Allah madaukaki Yana cewa a cikin Alkura' ni : { Allah Yana nufin sauƙi gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani gare ku } [ Suratul Al-Baqarah 185 ].

Misali: wajibi ne mutun ya yi sallah a tsaye, amma idan ba ya iyawa, sai ya yita a kwance, ko a sharen shi.

Kuma idan mutun yana cikin halin balaguro an ragonta masa ya hada sallar azahar tare da la'asr, haka ma magriba da isha'i, kuma duk sallah dake da raka'a hudu sai ya sallaceta raka'a biyu.

Kuma idan ya na cikin balaguro a cikin watan ramadana an bashi damar ajie azmi, sai bayan ramadana ya ramka daidai kwanakin da bai azunta ba, wannan kwa dan nema masa sauki ne.

Kuma shari'ar muslunci ba ta kama mutun da abin da aka tilasa shi a kai, ko kwa abin da ya yi da kuskure ko mantuwa ba;  Allah madaukaki Yana cewa a cikin Alkura' ni : { 286. Allah ba Ya kallafa wa rai fãce ikon yinsa, yana da lãdar abin da ya tsirfanta, kuma a kansa akwai zunubin abin da ya yi ta aikatãwa: « Yã Ubangijinmu! Kada Ka kãmã mu, idan mun yi mantuwa, ko kuma mun yi kuskure. Yã Ubangijinmu! Kuma kada Ka aza nauyi a kanmu, kamar yadda Ka aza shi a kan waɗanda suke a gabãninmu. Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu ɗaukar abin da bãbu ĩko gare mu da shi. Kuma Ka yãfe daga gare mu, kuma Ka gãfarta mana, kuma Ka yi jin ƙai gare mu. Kai ne Majibincinmu, sabõda haka Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai ».   [ Suratul Al-Baqarah 286 ].

5- yana daga ababen da suka sanya Alkura' ni mu'ajiza ne karantarwar Shi a kan halayya na gari, da yanda mutun zai tafi a cikin rayuwa ba tare da ya tsutu ba, ko ya tsutar.

Umarnin shi da karantarwar shi da ke kira ga rahma da son juna, tare halaye na gari, da taimakon juna,  suna da yawa. Mawadaci zai taimakawa mabukaci da wani kankanen rabo daga cikin dukiar sa da ake kira ( zakka ), idan kuma kyauta ce ta ganin dama ba wajibi ba ana kiran ta ( sadaka ).

Kai har fursinin yaki, muslunci ya yi umarni da a kyautata masa; domin Allah Ya yabi masu ciyar da shi;  Allah madaukaki Yana cewa a cikin Alkura' ni :  { 8. Kuma suna ciyar da abinci, a kan suna bukãtarsa, ga matalauci da marãya da kãmamme }.[ Suratul Al- insa'n ].

Daga misalen buwayar Alkura' ni ta bangaren karantar da kyawawan halaye a kwai fadar Allah mai girma: { 23. Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi, kum game da mahaifa biyu ku kyautata kyautatawa, ko dai ɗayansu ya kai ga tsũfa a wurinka ko dukansu biyu, to, kada ka ce musu 'tir' kuma kada ka tsãwace su kuma ka faɗa musu magana mai karimci. 
24. Kuma ka sassauta musu fikãfikan tausasãwa na rahama. Kuma ka ce: « Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka yi rẽnõna, ina ƙarami. » 
25. Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da yake a cikin rãyukanku. Idan kun kasance sãlihai to lalle ne shĩ Ya kasance ga mãsu kõmawa gare Shi, Mai gãfara. 
26. Kuma ka bai wa ma'abũcin zumunta hakkinsa da miskĩna da ɗan hanya. Kuma kada ka bazzara dũkiyarka, bazzarãwa. 
27. Lalle ne mubazzarai sun kasance 'yan'uwan shaiɗanu. Kuma Shaiɗan ya kasance ga Ubangijinsa, mai yawan kãfirci. 28. Ko dai ka kau da kai daga gare su dõmin nẽman rahama daga Ubangijinka, wadda kake fãtanta, to sai ka gaya musu magana mai laushi. 
29. Kuma kada ka sanya hannunka ƙuƙuntacce zuwa ga wuyanka, kuma kada ka shimfiɗa shi dukan shimfiɗãwa har ka zama abin zargi, wanda ake yanke wa. 
30. Lalle ne Ubangijinka Yanã shimfiɗa arzĩki ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuƙuntãwa. Lalle Shi, Yã kasance Mai sani ga bãyinSa, Mai gani. 
31. Kuma kada ku kashe 'yã'yanku dõmin tsõron talauci. Mu ne ke arzũta su, su da ku. Lalle ne kashe su yã kasance kuskure babba. 
32. Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya. 
33. Kuma kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da haƙƙi, kuma wanda aka kashe, yanã wanda aka zãlunta to, haƙĩƙa Mun sanya hujja ga waliyyinsa, sai dai kada ya ƙẽtare haddi a cikin kashẽwar. Lalle shĩ ya kasance wanda ake taimako. 
34. Kuma kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce dai da sifa wadda take ita ce mafi kyau, har ya isa ga mafi ƙarfinsa. Kuma ku cika alkawari. Lalle alkawari yã kasance abin tambayãwa ne. 
35. Kuma ku cika mũdu idan kun yi awo, kuma ku auna nauyi da sikẽli madaidaici. Wancan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara. 
36. Kuma kada ka bi abin da bã ka da ilmi game da shi. Lalle ne jĩ da gani da zũciya, dukan waɗancan ( mutum ) yã kasance daga gare shi wanda ake tambaya. 
37. Kuma kada ka yi tafiya a cikin ƙasa da alfahari. Lalle kai bã zã ka hũda ƙasa ba kuma bã zã ka kai a duwãtsu ba ga tsawo }. [ Suratul Al-Asra ].

6 – daga cikin ababen da ke tabbatar da mu'ajizar Alkura' ni a cikin shari' ar da ya zo da ita kasancewar ya yi watsi da dukkan abin da ya shafi kabilanci ko banbancin launi ko na harshe.

Alkura' ni ya yaki dukkan banbanci na launi, ko na harshe, ko na dangantaka, ko na kasa ko na kabila,  tsakanin mutane; abin da ke banbanta mutane shine tsoron Allah. Mutun yana daukaka ne da tsoron Allan shi, yana daukaka ne da halayen shi na gari, da mu'amala wadda take mai kyau. Wadannan kwa abubuwa ne wadanda ba su da alaka da launin fata, ko kwa wadata ko talauci.

Allah madaukaki Yana cewa a cikin Alkura' ni :  { 13. Yã kũ mutãne! Lalle ne Mũ, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangõgi da kabĩlõli, dõmin ku san jũna. Lalle mafĩfĩcinku daraja a wurin Allah, ( shĩ ne ) wanda yake mafĩfĩcinku a taƙawa. Lalle nẽ Allah Masani ne, Mai ƙididdigẽwa } [ Suratul Al-Hujurat ].

7 – yana kuma cikin manyan manyan huskokin mu'ajizar hukance hukuncen Alkura' ni kasancewar su sun kunshi maslahohi biyu wadanda dukkan mutane suke nema; sune: gamewa ( shar'ia ta shafi dukkan bangarorin rayuwa ) da kuma rishin barin wani bangare ya rinjayi wani bangare.

hukance hukuncen Alkura' ni sun shafi dukkan bangarorin rayuwa, ba tare da mance wani bangare ba.

Daga cikin misalai: za mu ga cewa sun shafi duniya da lahira.

Alkura' ni yana umarnin dan Adam ya raya ita wannan duniya da ya ke a cikin ta gini mai anfani, tare da cewa tunanin shi yana ga lahira ne; wannan kwa zai sa shi ya kasance mai gaskiya cikin dukkan abin da zai aikata , kuma ya kasance mai amana ne da kyawan mu'amala tare da mutane, kuma tunawarshi ga Allah zai sa ya kasance mai bauta ne ga Allah a ko wane lokaci; domin shirin saduwa da Ubangijinsa.

Allah mabuwayi da daukaka Yana cewa: { 77. « Kuma ka biɗã a cikin abin da Allah Ya bã ka, gidan Lãhira, kuma kada ka manta da rabonka daga dũniya. Kuma ka kyautata, kamar yadda Allah Ya kyautata zuwa gare ka, kuma kada ka nẽmi ɓarna a cikin ƙasa, lalle ne Allah bã Ya son mãsu barna } [ Suratul Al-Qasas 77 ].

Abu na biyu: Alkura' ni ya gama bukatu na gangar jiki da kuma bukatu na raid a hankali.

Umarnin Alkura' ni yana baiwa gangar jiki hakkin ta wajen barci da jin dadi da iyali, da hutu …, kamar yanda ya ke kula da bukatu na ruhi tamkar duba da lissafi a game da wannan kaunin; domin ya san wanene ya halicci ran shi. Kuma Alkura' ni yana umarnin dan Adan da ya kasance mai kyawawan dabi'u kamar gaskiya da adalci da biyayya ga iyaye, da sadar da zumunta, da amana, da kyauta. Kuma ya bude masa kofar tuba, dan ya komo ga Ubangijinsa idan har ya saba masa. Ya kuma masa alkawali da al – janna wadda fadinta ya fi fadin sammai da kassai, a cikin ta kuma akwai dukkan dangogin abin da rai ta ke bukata.

Tsarki ya tabbata ga wanda ya sanya dukkan wadannan hukunce hukunce na mu'ajiza a cikin Alkura' nin sa !

8 – yana daga buwayar Alkura' ni kasancewar sharenSa baya warware share; ma'anonin Sa ma su tafiya da juna ne, hukunce hukuncen Sa masu karfafa juna ne, ko wace sura tana gaskata 'yar uwarta ne, babu tubka da warwara a cikin Sa.

Inda Shi ba daga Allah ya ke ba, da ya kasance mai tubka da warwara, sharen Shi ya na warware share.

Allah madaukaki yana cewa: {  82. Shin, bã su kula da Alƙur'ãni, kuma dã yã kasance daga wurin wanin Allah haƙĩƙa, dã sun sãmu, a cikinsa, sãɓã wa jũnamai yawa? }.  [ Suratul Al-Nisa 82 ].

Ga misali za mu samu dukkan hukunce hukuncen Alkura' ni suna kira ne zuwa ga ginshikan imani guda shida, kuma dukkan su suna kira ne zuwa ga ginshikan muslunci guda biyar …

9  – yana daga ababen da suka sanya Alkura' ni mu'ajiza ne kasancewar hukunce hukuncen shi sun rufe hanyar dukkan barna ta hanyar tanadar ukuba da ladabtaewa ga wanda ya aikata laifi kamar kisa, da sata, da yada barna a ban kasa, sai mutane suka samu kwancin hankali dalilin wadannan ukubobi da muslunci ya tanada.

Kai hasali ma, bincike ya nuna cewa ta'addanci yana karfi a cikin kasashen da ba su tanadi ukuba ba ga 'yan ta'adda; domin su a guntuwar fahintar su suna ganin cewa – a tunanin su takaitacce - sun tausayawa dan ta'adda ne, ba tare da sun diba maslahar jama'a gaba daya ba.

Ba su yi dogon tsinkaye ba game da cewa barin mai barna tamkar kira ne ga na korai shima ya aikata ta'addancin; saboda ya ga mujirimi ya na aikata abin da ya ke so ba tare da wani abu ya tsaya gaban sa ba.

Amma alkura' ni ka diba yanda ya yi kakkausar suka misali a kan kisan rai wadda ba ta cancanci hakan ba.

Allah madaukaki yana cewa: { lalle ne wanda ya kashe rai bã da wani rai ba, ko ɓarna a cikin ƙasa, to kamar yã kashe mutãne duka ne, kuma wanda ya rãya rai, to, kamar yã rãyar da mutãne ne gabã ɗaya }  [ Suratul Al-Ma'idah 32 ].

Wanda ya kalli abin da muslunci ya tanada na hukunce hukunce gameda  sakautawa ma su laifuffuka, da abin da suka kunsa na adalci da rahma, da hikma, zai tabbatar da cewa lalle wannan Alkua' nin yana da mu'ajizar.

10 – kuma yana daga mu'ajizar Alkura'ni kasancewar hukunce hukuncen Shi sun kasance tsaka tsakiya ne; ba su wuce gona da iri ba, kamar yanda ba su kasa ba.

Ga misali: wasu kasashe sun wuce gona da iri, inda suka hana mutun ya mallaki dukiya, yayin da wasu suka manta da mabukaci; sai ya kasance su duka sun samu kanun su a cikin matsala da rishin koncin hankali; domin yawan sace sace, ko boren masu kudi sun addabi wadannan al – ummomi. Dan haka tsari na muslunci shi tsakiya ne tsakanin wadannan tsari guda biyu; bai hana tara dukiya ba ta hanya mai kyau, kamar yanda ya tanadi wani kaso wanda ba ya tsutawa mai dukiya, shine zakka wadda mai dukiya zai baiwa mabukaci. Wannan kwa yana sa ko wane bangare ya lamince dad an uwan sa, sai a samu koncin hankali cikin al – ummah.

Lalle kwa wadannan hukunce hukunce ma su kayatarwa, wadanda suka kai matuka wajen kyawo suna nuni ne ga cewa hakika Shi Alkura' ni daga Allah Ya ke.

Allah madaukaki yana cewa a cikin Alkura' ni : { 143. Kuma kamar wancan, Muka sanya ku al'umma matsakaiciya dõmin ku kasance mãsu bãyar da shaida a kan mutãne } [ Suratul Al-Baqarah 143  ].

A karshe :

Lalle girman Alkura' ni da buwayar Shi suna da fuskoki ma su yawan gaske, zaka kuma same su a kan harshen ko wane musulmi namiji ko mace, kuma ko da menene ya kebanta da shi na daga ilmi; wanda ya karanci kimiyar siyasa zai goda maka mu'ajizar Alkura' ni a bangaren siyasa, wanda ya karanci tattalin arziki zai goda maka mu'ajizar Alkura' ni a fannin tattalin arziki …

Duk da yawan huskokin mu'ajizar Alkura' ni ta bangaren hukunce hukuncen Shi wadanda su kara karfafa musulmi ga riko da Shi tare da kara son Shi a cikin zukatan su, wannan kwa ba wai saboda hukunce hukuncen Shi  da ba su sabawa hankali ba  kwai ba ne ba, a'a saboda maganar Ubangijin su ne wanda yake hukunta abin da ya so, su kuma bayin Sa ne.

Kaka ne kuma idan wannan ya hadu da ababe da suka gabata wadanda muslunci ya kebanta da sun a daga hukunce hukunce wadanda babba da karami, maza da mata, mai hukunci da wanda ake wa hukunci,  suka yarda da su yarda ta so ba yarda ta ki ba, a mtsayin kundi wanda ke tsara rayuwa, wannan kwa saboda tushen sa mai tsarki da girma ne, domin tushen sa daga Allah ne; lalle Shi maganar Allah Ubangijin halittu ne, Allah wanda ke Shi ne mamallakin kowa da kowa, Wanda Ya san dukkan abin da ke kyautata rayuwar bayin Sa da abin da ke tabbatar da maslahar su.

Yana da kyau bayan bayani a kan huskokin buwayar Alkura' ni, mu yi tunatarwa game da babban manufar sabkar da Alkura' ni; manufar nan ita ce: shiryar da mutane ga bautar Allah Shi kadai, ba tare da hada Shi da wani a cikin bauta ba. Wannan kwa ta hanyar bayani tare da hujjoji - wadanda ba su barin shakku tare da su – a kan kasancewar akwai Allah, kuma Shi kadai Ya yi halitta, kuma Shi kadai Ya mallake su, dan haka Shi kadai Ya cancanci a bauta masa, tare da tabbar masa da sunayen Sa da sifofin Sa, wadanda suka kai matuka wajen kyawo.

Wannan kwa shi ne manufar aiko da manzonni; Allah yana cewa a cikin Alkura' ni mai tsarki: { 170. Yã kũ mutãne! Haƙĩƙa, Manzo yã je muku da gaskiya daga Ubangijinku. Sabõda haka ku yi ĩmãni yã fi zama alhẽri a gare ku. Kuma idan kun kãfirta, to, Allah Yanã da abin da ke cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima } [ Suratul Al-Nisa ].

Allah Ya kuma ce: { 92. « Kuma inã karanta Alƙur'ãni. » To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai. Kuma wanda ya ɓãce, to, ka ce: « Ni daga mãsu gargaɗi kawai nake » } [ Suratul Al-Naml ].

Bayan haka, wannan littafin babu wani da zai iya zuwa da kwatankwacin Sa, kai ko da aljannu da mutane sun hada karfin su a kan su zo da kwatankwacin Sa ba za su iya zuwa da shi ba har abada; domin maganar Allah ne Shi, Ya sabkar da Shi ga manzon Shi Muhammad ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ), dan ya isar da Shi zuwa ga bayin shi, ya kuma yi wa wanda ya yi da'a alkawali da aljanna, wanda kwo ya bijire azabar wuta tana jiran shi.

Abubuwa suna bayyana ne da kishiyoyin su; dan haka ka diba halin mutane a yau; suna neman kwancin hankali da sa'ada, dan haka sun samarda dokoki da kundaye, amma tambayar da ta dimautar da su ita ce: wanene ke da hakkin sanya kundi ? mai hukunci ko wanda za ayi wa hukunci ?

Sai ya kasance amsar da za ta gamsar da bangarorin biyu ita ce: wadanda suka balaga su zabi wadanda za su wakilce su a majalisar dokoki, sai kuma 'yan majilisar su sanya dokokin nan da za'a hukunta !

To abin tambaya shine: duk wadanda suka cancanci shiga wannan majalisa sun shige shi ? ko kuma a kwai da yawa wadanda suke cancantar shigar shi wadanda ba su shiga ba; domin ba su yarda da tsarin zaben ba ?

Duk da haka wadannan da suka yarda suka shiga zaben za su gudanar da shi ba tare da wadanda ba su yarda ba, sa'an nan daya daga cikin jam'iyun siyasa sai ta lashe zaben da karamin rinjaye. Daga karshe sai ya kasance dukkan dokoki ana sanya su tare da la'akari da abin da yake gyara shi wannan bangare mai karamin rinjaye !

Shin za mu iya sifanta wannan dokoki da adalci ?! ko kuma da cewa suna kare maslahar kowa da kowa ?

Za mu barka ka baiwa kanka amsa ya kai makaranci , tare da la'akari da cewa so da yawa ake kawo gyaran huska ga wadannan dokoki, ba  dan kome ba said an tabbatar da maslahar wasu.

Sari'a ta Allah babu haka a cikin ta, ta zo ne saboda kowa da kowa, babu banbanci a cikin ta tsakanin mai mulki da wanda ake yiwa mulki, mai kudi da matlauci, ta Allah ce, tana diba maslahar kowa da kowa.

Wannan kuma yana tabbatar mana cewa 'yan Adam ba za su iya kawo wata shari'a ba wadda za ta iya tafiyar da al amurran su nay au da kullun ba, ba tare da zalunci da son rai ba, muddin wannan shari'a bata kasance tushenta daga Allah ne ba. Dan haka ne Allah ya saukar da littafin Sa na karshe, wanda ke shi ne Alkura' ni, wanda ya kunshi shari'a ta Ubangiji ga dukkan bayi, wanda kuma yake cike da huskoki na buwaya a cikin hukunce hukuncen Sa, ma su tabbatar wad an adam sa'ada da dadin kai a cikin rayuwar sa, a ko wane lokaci, a ko wane guri.

 

Ma rubuci : Bandar Ahmad